Sheikh Gumi Ya Tona Asirin Gwamnati, Ya Fadi Abin da Suka Sani kan Ta’addanci

Sheikh Gumi Ya Tona Asirin Gwamnati, Ya Fadi Abin da Suka Sani kan Ta’addanci

  • Malamin addini Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya yi tone-tone kan gwamnatin Najeriya game da ta'addanci a kasar
  • Gumi ya ce duk lokacin da yake ganawa da ‘yan bindiga, yana tafiya tare da jami’an tsaro kamar ‘yan sanda da sojoji
  • Malamin ya jaddada cewa tattaunawa da kungiyoyi masu dauke da makamai na iya taimakawa wajen warware matsalolin tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Ahmad Gumi, ya sake yin magana kan ta'addanci a Najeriya.

Sheikh Gumi ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta san sunayen ‘yan ta’adda da kuma wuraren da suke boye a sassa daban-daban na kasar.

Sheikh Gumi ya magantu kan ta'addanci a Najeriya
Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi. Hoto: Salisu Hassan.
Source: Facebook

Ta'addanci: Sheikh Gumi ya kalubalanci gwamnati

Malamin ya bayyana hakan ne yayin wata hira a wani bidiyo da Punch ta bibiya, wanda ya yadu a kafafen sada zumunta a ranar Talata 10 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

ICPC: Lauyan El Rufa'i ya yi martani kan 'gano' gidajen tsohon gwamna a kasar Masar

Gumi ya yi wannan bayani ne yayin da yake kare kansa kan zargin cewa yana ganawa da kungiyoyin ‘yan bindiga da ke addabar wasu sassan Najeriya.

Ya jaddada cewa ba ya zuwa irin wadannan tattaunawa shi kadai, domin yana tafiya tare da jami’an tsaro.

A cewarsa:

“Gwamnati ta san kowane dan ta’adda da suna da kuma inda yake. Ni ba na zuwa ni kadai domin yin sulhu, ina tafiya tare da ‘yan sanda, sojoji da sauran hukumomin tsaro.”
Gumi ya magantu kan ta'addanci da ya addabi Najeriya
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Martanin Gumi kan zargin alaka da ta'addanci

Gumi ya kuma mayar da martani kan zargin da ake yi masa cewa yana da alaka ta kusa da ‘yan ta’adda da miyagu da ke haddasa rikici a Najeriya.

Wasu masu sukar sa sun ce yana kare su ko kuma yana kokarin ganin an yi sulhu da su wanda mafi yawan mutane sun nuna shakku kan aminta da su.

Sai dai malamin ya ce a wasu lokuta yayin tattaunawar sulhu, ya kan ziyarci sarakunan gargajiya domin tattauna matsalar tsaro da neman dabarbaru kan dakile matsalar.

Ya kuma bayyana cewa a wasu lokuta har ya kan shiga cikin dazuzzuka inda ake zargin ‘yan bindiga ke boye domin yin irin wadannan tattaunawa, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amincewa Yarbawa su dauki 'yan sa kai don kare yankinsu daga 'yan ta'adda

A cewarsa:

“Na kan je wajen sarakuna. A wani lokaci ma lokacin da muka je wani daji, har da mata muka shiga cikin dajin.”

Sheikh Gumi ya dade yana kira da a yi tattaunawa da kungiyoyin dauke da makamai a Arewacin Najeriya domin nemo hanyar kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

Gumi ya ce Yajuju da Majuju sun bayyana

A baya, an ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa Yajuju da Majuju sun riga sun bayyana a duniy.

Rahoto ya nuna cewa malamin ya yi magana ne yayin gabatar da tafsirin Ramadan a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2026 a jihar Kaduna.

Sheikh Gumi ya yi magana ne yayin da ake cigaba da kashe-kashe a duniya, musamman bayan barkewar yakin Amurka da kasar Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.