'Yaƙi Ya Kare': Abin da Matawalle Ya Ce bayan Dauda Lawal Ya Koma APC

'Yaƙi Ya Kare': Abin da Matawalle Ya Ce bayan Dauda Lawal Ya Koma APC

  • Karamin ministan tsaro na ƙasa, Bello Matawalle, ya yi magana bayan shigowar Gwamna Dauda Lawal Dare APC mai mulki
  • Matawalle ya yaba sauyin sheƙar Gwamnan Zamfara daga jam’iyyar PDP zuwa APC da ke mulkin Najeriya
  • Dauda ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’i da suka addabi PDP ne suka sa ya fice daga jam’iyyar, yana mai cewa ya samu goyon bayan masu ruwa da tsaki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi martani bayan Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya koma APC.

Matawalle ya yaba matakin da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ɗauka na sauya sheƙa daga PDP zuwa APC mai mulki.

Matawalle ya yi maraba da zuwa Dauda Lawal
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da gwamna Dauda Lawal. Hoto: Dr. Bello Matawalle, Dauda Lawal.
Source: Twitter

Da yake martani, Matawalle ya ce shigan gwamnan APC wani babban tarihi ne a siyasar Zamfara kuma ya yi masa maraba da shiga jam’iyyar, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

"Gaskiyar dalilin da ya sa na bar PDP na shiga APC," Gwamna Dauda ya yi bayani

Dalilin shigan Gwamna Dauda Lawal APC

Lawal, wanda ya gaji Matawalle a matsayin gwamnan Zamfara, ya fice daga PDP bayan kotun daukaka ƙara a Abuja ta tabbatar da hukuncin babbar kotu.

Hukuncin ya hana jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da aka yi a Ibadan ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025.

Ya bayyana cewa hukuncin kotun daukaka ƙara ya kawo ƙarshen zaman da ya yi a PDP, bayan ƙoƙarin sasanta rikicin jam’iyyar bai yi nasara ba.

Lawal ya ce shiga APC zai taimaka wajen ci gaba da manufar ceto da sake gina Zamfara, yana mai cewa shawarar ta samu goyon bayan masu ruwa da tsaki.

Matawalle ya sha alwashin kawo zaman lafiya a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da Gwamna Dauda Lawal ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da Matawalle ya ce kan Dauda Lawal

Matawalle ya ce yanzu Lawal ya shiga cikin masu ci gaba, yana mai cewa za su hada kai domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya da ci gaban Zamfara.

Ministan ya kara da cewa jihar na bukatar hadin kai domin tinkarar matsalolin tsaro tare da aiwatar da manufofin gwamnatin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Gwamna Dauda Lawal ya bi sahun Abba Gida Gida, ya sauya sheka zuwa APC

Ya ambaci cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna siyasa ba yaƙi ba ce, illa hanya ce ta gina hadin kai duk da bambance-bambance, cewar Daily Post.

Ministan ya ce dawowar Lawal APC wani irin haduwar siyasa ce a tsakaninsu, yana mai bayyana shi a matsayin aboki kuma dan uwa.

Ya kuma bukaci dukkan ‘yan APC a Zamfara su hada kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben shekarar 2027.

A zaben gwamnan Zamfara na 2023, Lawal na PDP ya samu kuri’u 377,726 inda ya doke Matawalle na APC wanda ya samu kuri’u 311,976.

Matawalle ya magantu kan tazarcen Tinubu

Mun ba ku labarin cewa karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaben 2027.

Matawalle ya ce manufofin Tinubu sun fara haifar da daidaiton tattalin arziki, inganta tsaro da karfafa cibiyoyin gwamnati musamman a Arewa.

Ya gargadi ‘yan siyasa masu shirya rikici da cewa burinsu na kashin kai na iya lalata dimokuradiyya, yana kira da a goyi bayan shirye-shiryen gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.