Wasu Mutane Sun Dasa Bam a Fitaccen Masallaci a Maiduguri? Gaskiya Ta Fito
- Masallacin Malam Bako dake Borno ya kawo karshen jita-jitar da ake yadawa a soshiyal midiya cewa wasu mutane sun dasa bam a harabarsa
- A cikin wata sanarwa, hukumar gudanarwar masallacin ta tabbatar da cewa masallacin da al'ummar da ke kewaye da shi na cikin aminci
- Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta yi kira ga mazauna birnin Maiduduri da su guji yada labaran karya wadanda ke tada hankulan al'umma
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Borno - Hukumar gudanarwar masallacin Malam Bako dake birnin Maiduguri, jihar Borno, ta karyata rahotannin dake yawo a dandalin sada zumunta dake iƙirarin cewa wasu mutane sun dasa bam a masallacin.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yau Talata, ta bayyana waɗannan rahotanni a matsayin ƙarya marasa tushe waɗanda ake yadawa ne kawai don tada hankalin jama'a.

Source: Facebook
An karyata rahoton dasa bam a masallaci
Sanarwar, mai taken "Sanarwa daga hukumar gudanarwar masallacin Malam Bako, Layin Hadiza," ta tabbatar da cewa masallacin da daukacin unguwar dake kewaye da shi suna cikin kwanciyar hankali da tsaro, in ji rahoton Punch.
Hukumar ta yi kira ga jama'a da su daina yaɗa bayanan da ba a tantance ba waɗanda za su iya haifar da fargaba da tsoro a tsakanin al'umma yau.
Wani Shamsuddeen Ahmed Tijjani, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:
"Shugabannin masallacin Malam Bako da ke Layin Hadiza, Maiduguri, suna sanar da jama’a cewa saƙon da yake yawo a kafafen sada zumunta wanda ke cewa wasu mutane sun zo domin dasa bam a cikin masallacin ƙarya ne gaba ɗaya kuma ba shi da tushe.
"Muna sanar da kowa a sarari cewa ba a samu irin wannan lamari ba a cikin masallacin ko a kewaye da shi. Masallacin da unguwar da ke kewaye da shi suna cikin kwanciyar hankali da tsaro.
'Saboda haka muna roƙon jama’a da su yi watsi da wannan saƙo, kuma su guji yaɗa labaran da ba a tabbatar da su ba, domin hakan na iya haifar da tsoro da firgici a cikin al’umma ba tare da dalili ba.
"Allah Ya ci gaba da kare al’ummarmu kuma Ya ba mu zaman lafiya da tsaro. Amin."
Ƴan sanda sun gargadi masu farfaganda
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Borno, Nahum Daso, ya tabbatar da cewa rahoton dasa bam a masallacin ba shi da tushe.

Source: Original
Daso ya bukaci mazauna birnin Maiduguri da su kasance masu sa ido sosai kan duk wani abu da ba su amince da shi ba, tare da gujewa yaɗa labaran ƙarya waɗanda ka iya taɓa zaman lafiyar jihar.
Wannan tsoro ya samo asali ne sakamakon ƙaruwar ƙalubalen tsaro a jihar, ciki har da harin bam da aka kai a masallacin Al-Adum dake yankin kasuwar Gamboru a watan Disambar bara, inda mutane biyar suka mutu.
Ganin yadda dakarun Boko Haram suka kai hare-hare kwanan nan a yankunan Gwoza da Ngoshe, hukumomi na ƙara ƙarfafa matakan tsaro a wuraren ibada da sansanonin soji domin kare rayukan fararen hula yau.
Bam ya tashi da mutane a masallaci
Tun da fari, kun ji cewa, wani abin fashewa (IED) da ake kyautata zaton bam ne ya tashi da mutane a masallaci ana cikin sallar Magariba a jihar Borno.
Rahotonni sun nuna cewa wani dan kunar bakin wake ne ya tashi bam din da misalin karfe 6:00 na yammaci a wani masallacin Gamboru a Maiduguri.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa masallacin na tara mutane da dama a kullum, ciki har da ’yan kasuwa da masu sayar da kaya da ke harkokinsu a Kasuwar Gamboru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


