Yadda 'Yan Boko Haram Suka Kashe Kwamandojin Sojoji 3 cikin Sati 1 a Borno

Yadda 'Yan Boko Haram Suka Kashe Kwamandojin Sojoji 3 cikin Sati 1 a Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya sun rasa wasu manyan kwamandoji a hannun 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
  • A cikin sati daya, dakarun sojoji sun rasa kwamandoji uku sakamakon hare-haren da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai masu
  • Asarar rayukan kwamandojin na zuwa ne yayin da dakarun sojoji ke ci gaba da matsa lamba ga 'yan ta'addan Boko Haram

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Rundunar sojin Najeriya ta rasa aƙalla manyan kwamandoji uku biyo bayan hare-haren da Boko Haram da ISWAP a jihar Borno.

'Yan ta'addan sun hallaka kwamandojin ne bayan da suka kai hare-hare a wurare daban-daban cikin kwanaki bakwai a jihar Borno.

Sojojin Najeriya sun rasa kwamandoji a Borno
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce sababbin asarar rayukan sun kawo adadin manyan kwamandoji bakwai da kuma Janar ɗaya (Birgediya Janar) da aka kashe a cikin watanni uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

Shiri ya yi: Dakarun sojoji sun yi bajinta, sun kashe babban kwamandan ISWAP

'Yan Boko Haram na kai hare-hare a Borno

Masu lura da al'amura da na tsaro sun ce hare-haren baya-bayan nan sun nuna irin barazanar da ’yan tada ƙayar baya ke ci gaba da yi a Borno duk da ayyukan sojoji da ake ci gaba da yi da nufin gurgunta ƙarfinsu.

A cikin watannin baya-bayan nan, sojoji sun tsananta ayyukansu a wurare masu haɗari, ciki har da Dajin Sambisa, Timbuktu Triangle, Tuddan Mandara da kuma Yankin Tafkin Chadi.

Sanarwar sojoji ta nuna cewa ana kashe daruruwan kwamandojin ’yan tada ƙayar baya da mayaka yayin ayyukan da ake gudanarwa a wurare daban-daban, tare da lalata manyan sansanonin ta’addanci da dama.

Kwamandojin sojojin da aka kashe

Bisa rahotannin kafafen yaɗa labarai, manyan kwamandoji ukun da aka kashe kwanan nan su ne Major U.I. Mairiga, wanda ya jagoranci sansanin Mayenti; Lt-Col Umar Faruq, kwamandan sansanin Kukawa da kuma runduna ta 101 Brigade; da kuma Lt-Col S.I. Iliyasu, wanda ya yi aiki a Konduga.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a sun yi wa Amurka raddi, za su fito kan titunan Abuja

Bincike ya nuna cewa akasarin mace-macen sun faru ne yayin hare-hare kan sansanonin sojoji ko kuma kwanton ɓauna da ’yan tada ƙayar baya suke yi lokacin ayyukan kakkabe 'yan ta'adda.

Lamari na baya-bayan nan ya faru ne a ranar Litinin, 9 ga Maris 2026, lokacin da ’yan ta'ada suka mamaye wani sansanin sojoji a ƙaramar hukumar Kukawa ta Borno, inda suka kashe babban kwamanda, Lt-Col Umar Faruq, tare da sojoji da dama.

Jaridar The Cable ta ce majiyoyin tsaro sun ce ’yan tada ƙayar bayan sun kai hari sansanin ne da misalin karfe 12:00 na dare.

Kakakin rundunar haɗin gwiwa ta yankin Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, Lt-Col Sani Uba, ya tabbatar da cewa an kashe wani jarumin jami’i a harin amma bai bayyana ko wane ne ba.

'Yan Boko Haram sun kashe kwamanda

A watan da ya gabata, ’yan ta'adda sun taɓa kai hari sansanin sojojim amma dakarun da ke ƙarƙashin jagorancin marigayi Lt-Col Umar Faruq suka fatattake su, inda rahotanni suka ce an kashe ’yan ta’adda da dama.

A ranar 1 ga Maris, 2026, aka kashe wani babban kwamandan, Manjo Umar Ibrahim Mairiga, lokacin da ’yan ta’addan Boko Haram suka kai hari sansaninsa da ke Mayenti, ƙaramar hukumar Bama.

Kara karanta wannan

Babu sauki: Mayakan Hezbollah sun yi wa sojojin Isra'ila kwanton bauna, sun yi masu illa

Wata majiyar tsaro ta ce jami’in ya nuna jarumta wajen dakile harin amma daga ƙarshe aka rinjaye shi.

“Kwamandan sansanin, Manjo U.I. Mairiga, ya yi gumurzu sosai da ’yan ta’addan amma daga ƙarshe aka rinjaye shi bayan wasu sojojinsa sun tsere cikin daji.”

- Wata majiya

'Yan Boko Haram sun hallaka kwamandojin sojoji a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kashe kwamanda tare da sojoji

A ranar 6 ga Maris 2026, an kashe babban kwamandan bataliya ta 222 da ke Konduga, Lt-Col S.I. Iliyasu, tare da sojoji da dama yayin wani harin na ’yan ta’addan Boko Haram.

Tun da fari, a ranar 28 ga Janairun 2026, mayakan Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin sojoji a Damasak, inda suka kashe sojoji bakwai, ciki har da babban kwamandan.

Ya kamata gwamnati ta tashi tsaye

Wani mazaunin Borno, Babagana Bukar, ya nuna damuwa kan yadda ake rasa dakarun tsaro a hannun 'yan ta'adda.

"Akwai damuwa matuka kan yadda ake rasa dakarun sojoji a hannun tsagerun 'yan ta'addan Boko Haram."
"A cikin sati daya an rasa kwamandojin da ke jan ragamar sojoji da dama, wannan abin tashin hankali sosai"

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe babban kwamandan sojoji a Borno

"Ya kamata gwamnati ta kara azama wajen samar da isassun kayan aiki ga dakarun sojoji ta yadda za su iya yin nasara kan 'yan ta'adda."

- Babagana Bukar

An yi jana'izar sojojin da aka kashe

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rundunar sojojin Najeriya ta yi jana'izar wasu daga cikin jami'anta da aka kashe a fagen daga.

An gudanar da jana’izar ne a makabartar sojoji da ke Maimalari Military Cantonment a Maiduguri, babban birnin jihar.

Da yake jawabi yayin jana’izar, kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya bayyana cewa akwai radadi rasuwar jami'an tsaron.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng