Bayan Jawo Tashin Fetur, Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ya Kara Jefa 'Yan Najeriya a Matsala

Bayan Jawo Tashin Fetur, Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ya Kara Jefa 'Yan Najeriya a Matsala

  • Ana ci gaba da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kan kasar Iran
  • Rikicin da ake yi ya jawo tashin farashin gangar danyen mai wanda hakan ya sanya aka samu karuwar kudin man fetur a Najeriya da wasu kasashe
  • Tuni dai tashin farashin mai ya jawo tasiri ga tattalin arzikin Najeriya inda mutane suka fara ji a jikinsu daga uwa duniya

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Rikicin Gabas ta Tsakiya ya fara yin tasiri ga tattalin arzikin Najeriya yayin da tashin farashin ɗanyen mai a duniya ke janyo hauhawar farashin fetur.

Karuwar farashin danyen mai ya haifar da ƙarin kuɗin sufuri da farashin abinci a sassa daban-daban na ƙasar.

Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabe
Wasu motoci yayin sayen man fetur a gidan mai Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ce a manyan biranen ƙasar, da suka haɗa da Legas, Abuja, Kano, Kaduna, Port Harcourt, da Yenagoa, masu ababen hawa da matafiya na fama da sabon sauyin farashin fetur.

Kara karanta wannan

Fetur ya kara tsada: Yadda yakin Iran ya jawo farashin gangar mai ya haura $100

Kudin fetur ya yi tashin gwauron zabi

Farashin lita ɗaya na man fetur ya tashi zuwa tsakanin N1,020 da N1,100 a gidajen mai da dama.

Wannan yanayi ya tada hankalin mutane, masu harkar sufuri, da ’yan kasuwa, waɗanda ke fargabar cewa ƙarin na iya tsananta tsadar rayuwa wadda aka riga aka daɗe ana fama da ita, sannan ya ƙara matsa wa kasafin kuɗin iyalai.

A Legas, matafiya da iyalai sun ce tuni suka fara kashe kuɗi masu yawa wajen sufuri da sayen kayan abinci biyo bayan sabon ƙarin farashin man fetur ɗin.

Binciken Legit Hausa a ranar Litinin, 9 ga watan Maris 2026 ya nuna cewa a gidajen mai da dama a yanzu ana sayar da fetur tsakanin N1,050 zuwa N1,100 a kowace lita, dangane da gidan man.

Farashin kayan abinci ya tashi

Ana kuma jin tasirin ƙarin farashin man a kasuwannin abinci a wasu garuruwan Legas, inda kuɗin jigilar kayan gona ya tura farashin kayayyaki sama.

Kara karanta wannan

Trump na tsakiyar yaki da Iran: Bam ya tarwatse a wani ofishin jakadancin Amurka

’Yan kasuwa sun bayyana cewa farashin tattasai da tumatir ya tashi sosai cikin ƙanƙanin lokaci, inda suka ɗora alhakin hakan kan tsadar kuɗin sufuri.

Yanzu ana sayar da ƙaramin buhun tattasai a kan kusan N82,000, idan aka kwatanta da N18,000 da ake sayarwa a baya.

Matsakaicin buhu ya tashi zuwa kusan N122,000 daga N22,000, yayin da babban buhu yanzu farashinsa ya kai kusan N172,000 idan aka kwatanta da kusan N70,000 a baya.

Haka zalika, farashin tumatir ya yi tashin gwauron zaɓi yayin da ƙaramin kwando da ake sayarwa a kan N22,000 a baya, yanzu ya kai kusan N50,000, yayin da babban kwando ya tashi daga kusan N62,000 zuwa N125,000.

Farashin tumatir ya tashi a kasuwannin Legas
Kwandunan tumatir wanda ake sayarwa a kasuwa Hoto: @ejykmykel1
Source: Twitter

Masu sayar da abinci sun fara kokawa

Masu sayar da abinci ma sun fara jin matsin lamba daga tsadar man fetur.

A kasuwar Swali da ke Yenagoa, ’yan kasuwa sun ce farashin wasu kayan abinci, musamman kifi, ya tashi.

Madam Evilyn Tamuno, mai sayar da kifi a kasuwar, ta bayyana cewa ayyukan kamun kifi sun dogara ne kacokan kan kwale-kwale masu injinan da ke amfani da fetur.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare; Yakin Iran, Isra'ila da Amurka ya haifar da matsala a Najeriya

“Idan farashin mai ya tashi, masunta za su ƙara farashin kifi."

- Madam Evilyn Tamuno

Matatar Dangote za ta samar da fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote ta ba 'yan Najeriya tabbacin samar da isashshen man fetur yayin da ake ci gaba da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Matatar Dangote ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za ta ba da fifiko wajen samar da mai a cikin gida domin hana fuskantar karancin man fetur.

Ta bayyana cewa tana nan daram kan alkawarinta na kasancewa ginshikin daidaita kasuwar makamashi ta Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng