Tashin Hankali: Sunan Jigon APC Ya Fito cikin Masu Hannu Dumu Dumu a Kisan Sarki
- Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana matukar kaduwa kan zargin cewa wani jigon ta a Ebonyi na da hannu a sacewa da kashe wani basarake
- Majiyoyi suka ce ana zargin dan APC na da alaka da garkuwa da kisan mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar Ebonyi
- Shugaban APC a jihar, Stanley Okoro-Emegha, ya ce ba za su lamunci irin wannan mugun aiki ba, kuma za su goyi bayan adalci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abakaliki, Ebonyi - Jam’iyyar APC a jihar Ebonyi ta yi magana kan zargin jigonta da hannu a kisan basarake bayan yan bindiga sun yi garkuwa da shi.
APC ta ce ta shiga matukar kaduwa bayan samun rahoton cewa wani mambanta na da hannu a sacewa da kuma kisan Francis Igwe, mahaifin tsohon mataimakin gwamnan Ebonyi, Kelechi Igwe.

Source: Twitter
Premium Times ta ruwaito cewa rahotannin da aka tabbatar sun nuna cewa sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar na da hannu a lamarin.
Kisan Sarki: APC ta kadu kan zargin jigonta
Shugaban APC a jihar Ebonyi, Stanley Okoro-Emegha, ya bayyana kaduwarsa lokacin da ya jagoranci tawagar jam’iyyar zuwa ziyarar jaje ga iyalan marigayin a garin Ndufu-Alike da ke ƙaramar hukumar Ikwo.
Okoro-Emegha ya ce labarin cewa wani jigo a jam’iyyar na da hannu a kisan basaraken ya ba shi mamaki matuka, har ya kasa fitowa ya fuskanci jama’a cikin kwanaki biyun da suka gabata.
Ya ce:
“Wannan rahoto abin mamaki ne ƙwarai, domin cikin kwanaki biyu da suka wuce ban ma samu ƙarfin halin fuskantar jama’a ba.
“Mambobin jam’iyyar ba za su taɓa yarda ba cewa jam’iyyarmu za a danganta ta da irin wannan aiki ba.
“Muna gudanar da harkokinmu a matsayin yan uwa, har ma wani zai iya tsaya wa wani ya bada shaida duk da bambance-bambancen siyasa.”

Source: Original
Matsayar APC kan zargin jigonta a Ebonyi
Shugaban jam’iyyar ya jaddada cewa APC za ta goyi bayan duk matakin da gwamnatin jihar za ta ɗauka domin tabbatar da an yi wa iyalan Igwe adalci.
Ya ce gwamnan jihar, a matsayinsa na jagoran jam’iyya da kuma uban jihar, ba zai amince da irin wannan mugun aiki ba, komai matsayin wanda ake zargi.
A nasa ɓangaren, sakataren fadar yankin, Johnson Aloh, ya gode wa jam’iyyar bisa ziyarar jaje, yana mai cewa al’umma da fadar sun yi matukar alhini kan wannan lamari.
Ya ce abin ya girgiza su matuka ganin cewa sunan jam’iyyar da suke so ya gurɓace sakamakon aikin mutum ɗaya, cewar Channels TV.
Yadda aka sace basarake a Ebonyi
A baya, an ji cewa wasu ‘yan bindiga sun yi ta'asa bayan tabbatar da cewa sun sace Francis Igwe, mahaifin tsohon mataimakin gwamnan Ebonyi.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa coci, inda ‘yan bindiga kan babur suka tare motarsa.
Shugaban Ikwo, Sunday Nwankwo, da ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, suna cewa ana kokarin ceto dattijon cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng

