Ana Shirin Daukar Matasa 28,000 Aiki, Tinubu Ya Kara Albashin Sojojin Najeriya

Ana Shirin Daukar Matasa 28,000 Aiki, Tinubu Ya Kara Albashin Sojojin Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da karin albashi ga dakarun sojojin Najeriya da kuma alawus na musamman ga jami'an dake gadin Aso Rock
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan an samu rahoton cewa Tinubu ya amince a dauki sababbin sojoji 28,000 don karfafa tsaro a fadin Najeriya
  • Rundunar sojin Najeriya za ta tura jirage masu saukar ungulu zuwa jihar Benuwai domin taimakawa a wajen fatattakar 'yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Babban Hafsan Sojan Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙarin albashi ga dukkan jami'an rundunar sojojin Najeriya.

Janar Shaibu ya bayyana hakan ne a daren ranar Asabar, 7 ga Maris, lokacin buɗa baki da aka yi a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin sunaye da kasashen da Tinubu ya tura sababbin jakadun Najeriya

Shugaba Tinubu ya amince a kara albashin sojojin Najeriya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na karbar sarawa daga sojojin Najeriya. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Tinubu ya kara albashin sojojin Najeriya

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar sababbin kafofin sada zumunta, Olusegun Dada ne ya wallafa bidiyon jawabin Shaibu a shafinsa na X.

Laftanal Shaibu ya ce Tinubu ya kuma amince da ƙarin alawus-alawus ga dakarun dake gadin fadar shugaban ƙasa domin nuna jin daɗi ga ƙwazonsu.

A cikin jawabin nasa, Janar Shaibu ya gode wa shugaban ƙasar, wanda ya siffanta shi da "mai aiki tukuru", tare da jaddada cikakkiyar biyayya da sadaukarwar dakarun soji ga babban kwamandan nasu.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji ke fuskantar ƙalubalen tsaro daban-daban a faɗin ƙasar, inda ƙarin albashin zai zama kwarin gwiwa ga dakarun dake fagen fama.

Ɗaukar sababbin sojoji 28,000

Baya ga batun albashi, Laftanar Janar Waidi Shaibu ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya amince da ɗaukar sababbin dakarun sojoji guda 28,000 tare da ba su horo a cikin shekara ɗaya, in ji rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi karatun ta natsu, ya gano abin da ya assasa talauci a Najeriya

Janar ɗin ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara ga gwamnan jihar Benuwai, Rev. Fr. Hyacinth Alia, a birnin Makurdi.

Ya bayyana cewa daukar sababbin dakarun sojojin zai taimaka ne wajen toshe giɓin dake akwai a tsarin tsaron ƙasar nan.

Laftanal Janar Waidi Shaibu ya ce Tinubu ya amince a kara wa sojoji albashi.
Laftanal Janar Waidi Shaibu ya na magana a zauren majalisar dattawan Najeriya. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Inganta ayyukan sojoji a jihar Benuwai

Haka kuma, rundunar sojin ƙasar tana faɗaɗa sashen sufurin jiragen sama, inda aka tsara samar da jirage masu saukar ungulu ga rundunar "Operation Whirl Stroke" dake Jihar Benuwai.

Wannan zai taimaka wajen kai ɗaukin gaggawa da kuma fatattakar ƴan ta'adda cikin ƙanƙanin lokaci.

Janar Shaibu ya tabbatar wa mazauna jihar Benuwai cewa sojoji za su ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

Kalli bidiyon a kasa:

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan ta'addan Boko Haram ne sun kaddamar da munanan hare-hare kan sansanin sojoji da na 'yan gudun hijira dake garin Ngoshe a Borno.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa maharan sun mamaye sansanin sojoji na "82 Division TF Battalion" tare da ragargazar dakarun dake wurin.

An gano gawarwakin sojoji tara daga cikin wadanda aka kashe. Haka kuma, maharan sun kona tankunan yaki da motocin soji tare da sace makamai masu tarin yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com