Malaman Musulunci Sun Sauke Alkur’ani, Sun Goyi bayan Tazarcen Gwamna a 2027

Malaman Musulunci Sun Sauke Alkur’ani, Sun Goyi bayan Tazarcen Gwamna a 2027

  • Hadakar kungiyoyin Musulmi a jihar Taraba sun ayyana goyon bayansu ga gwamna Agbu Kefas domin ya sake tsayawa takara
  • Malamai sun yaba da matakin gwamnan na warware rikicin da ya shafi Musulmi a karamar hukumar Donga tare da kokari wajen inganta ilimi, tsaro
  • Mataimakin gwamnan a bangaren harkokin addinin Musulunci, Hon. Hussaini Ismail shi ya tabbata da haka ga wakilin Legit Hausa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Hadakar wasu kungiyoyin Musulmi a jihar Taraba ta bayyana goyon bayansu ga gwamnan jihar, Agbu Kefas.

Musulman sun bayyana aniyarsu ta goyon bayan gwamnan domin ya sake tsayawa takara karo na biyu a shekarar 2027.

Malaami sun sauke Alkur'ani ga gwamna Kirista
Hadimin gwamna Agbu Kefas, Hon. Hussaini Ismail da Musulmai da suka yi addu'o'i gwamnan. Hoto: Hussaini Ismail.
Source: Facebook

Mai taimakawa gwamnan a bangaren harkokin addinin Musulunci, Hon. Hussaini Isma'il shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a yau Lahadi 8 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Martanin malaman addini 5 game da yaƙin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya

Musulman Taraba sun yi addu'o'i ga Gwamna Kefas

An sanar da wannan goyon baya ne yayin wani zaman addu’a na musamman da aka gudanar domin neman zaman lafiya, hadin kai da kuma nasarar gwamnatin gwamnan a masallacin Juma'a na Saurara.

Zaman addu’ar, Hon. Hussaini Ismail ya jagoranta, ya samu halartar dimbin Musulmi daga kungiyoyi daban-daban a fadin jihar.

A yayin taron, masu ibada sun yi addu’o’i na musamman ga gwamna Kefas tare da bayyana goyon bayansu ga aniyarsa ta sake tsayawa takara karo na biyu.

An yi addu'o'in samun nasarar gwamna Kirista a zaben 2027
Hadimin gwamnan Taraba, Hon. Hussaini Ismail yayin addu'o'i ga Gwamna Agbu Kefas. Hoto: Hussaini Ismail, Agbu Kefas.
Source: Facebook

Jawabin Hon. Hussaini ga Musulmin Taraba

Da yake jawabi a wajen taron, Ismail ya yaba da matakin gaggawa da gwamnan ya dauka wajen warware rikicin da ya shafi al’ummar Musulmi a karamar hukumar Donga a baya-bayan nan.

Ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa matakin gwamnan a matsayin wani kokari na dawo da zaman lafiya, karfafa hadin kai da kuma inganta ci gaba a fadin jihar.

Ismail ya kara da cewa gwamnatin Kefas na ci gaba da aiwatar da shirye-shirye da nufin inganta rayuwar jama’a, musamman a bangarorin ilimi, tsaro da kuma ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Malamai sun nuna kishi, sun goyi bayan 'dan APC domin samun Musulmin gwamna

Haka kuma ya bukaci Musulmi su ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya, kauna da fahimtar juna, yana mai jaddada cewa hadin kan al’ummar jihar na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya da ci gaba mai ma’ana.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Taraba da su mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnatin da ke kan mulki baya domin samun cigaba da bunkasar jihar baki daya.

Wasu malaman Musulunci da mahalarta zaman addu’ar sun kuma nuna gamsuwarsu da salon shugabancin gwamna Kefas, inda suka ce wasu daga cikin shirye-shiryen gwamnatin tuni sun fara kawo sauyi mai kyau a fadin jihar.

Sun yabawa gwamnan musamman da amincewar da ya bayar na ware kudi N300m domin gina masallatai ga kungiyoyin Izala a Jos da Kaduna, reshen jihar Taraba, da kuma na Darika.

Taron ya kare ne da addu’o’i na musamman domin dorewar zaman lafiya, hadin kai da wadata a jihar Taraba da ma daukacin Nigeria.

Malamai sun yi wa Gwamna Kefas addu'i'o

A baya, mun ba ku labarin cewa a ranar Asabar 4 ga watan Janairun 2024 aka gudanar da addu'o'i na musamman ga Gwamna Agbu Kefas da jihar Taraba.

Kara karanta wannan

"Kada a dagula siyasar Kano": NNPP ta aika sako kan shirin tsige Mataimakin gwamna

An gudanar da addu'o'in ne a Masallacin Juma'a na Saurara da ke birnin Jalingo domin taimakawa gwamnan samun nasarori a mulkinsa.

Hakan ya biyo bayan yabawa da ayyukan alheri da Gwamna Kefas ke yi inda suka yi masa addu'o'in samun nasara a mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.