Katsina: Sojoji Sun Hallaka Yan bindiga 45, Hatsabiban Jagorori 2 Sun Sheka Barzahu
- Rundunar sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 45 a karamar hukumar Danmusa, Katsina bayan gumurzu mai zafi
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa daga cikin su akwai fitaccen jagoran ‘yan bindiga da ya addabi al'ummar jihar
- Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai hari Alhazawa a Musawa inda suka sace shanu, amma mazauna gari da wasu tubabbun ‘yan bindiga suka dakile su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Sojojin rundunar Najeriya sun kashe akalla ‘yan bindiga 45 bayan wata arangama mai zafi da ta faru a karamar hukumar Danmusa a Katsina.
Majiyoyin tsaro sun ce farmakin ya biyo bayan sahihin bayanan sirri da suka nuna ‘yan bindigar na kai hare-hare.

Source: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ta tabbatar da cewa daga cikin ‘yan bindigar da aka kashe akwai wasu manyan kwamandoji biyu.
Kwamandojin yan bindiga da aka hallaka
Majiyoyi suka ce manyan yan bindiga sun hada da Kachallah Alti, wanda ake cewa dan’uwan jagoran ‘yan bindiga Adamu Alieru ne da Kachallah Damale.
Rahotanni sun ce Alti shi ne mataimakin kwamanda ga Alieru, yayin da wani jagoran ‘yan bindiga mai suna Damale shi ma ya mutu a arangamar.
Rahotanni sun ce rikicin ya fara ne bayan ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kauyen Alhazawa a Musawa ranar 5 ga Maris, 2027.
A yayin harin, an ce ‘yan bindigar sun sace shanu daga hannun mazauna yankin, lamarin da ya janyo fargaba da tashin hankali a cikin al’ummar yankin.
Sai dai mazauna yankin tare da wasu tubabbun ‘yan bindiga sun yi yunkurin dakile harin, inda suka kashe ‘yan bindiga hudu tare da kwato shanun.
Bayan haka an mayar da shanun da aka kwato ga masu su, abin da ya kawo sauki ga mutanen da harin ya shafa.
Sai dai rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun sake taruwa washegari, ranar 6 ga Maris 2026 domin kai wani sabon hari na ramuwar gayya.

Kara karanta wannan
Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Source: Original
Yawan 'yan bindiga da aka hallaka a Katsina
A sakamakon wannan arangama, sojojin sun kashe ‘yan bindiga 45 tare da tarwatsa sauran da suka tsere zuwa dazuka.
Sai dai rundunar sojojin ta yi asara yayin arangamar domin bayan kashe sojoji uku a yayin fafatawar da aka yi da ‘yan bindigar.
Bincike ya nuna cewa Alti ya fara taka muhimmiyar rawa a cikin kungiyar ‘yan bindigar bayan rasuwar dan uwansa Kachalla Dan Isihu.
'Dan Isihu dai an kashe shi a baya yayin wasu hare-haren da jami’an tsaro suka kai domin dakile ayyukan ‘yan bindiga a yankin.
Rahotanni sun ce Alti ya shirya hare-hare masu yawa a wasu al’ummomi musamman a yankin Danjibga a karamar hukumar Tsafe ta Zamfara.
'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
Mun ba ku labarin cewa an sake samun hare-haren ‘yan bindiga a Kankara duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba wa hannu kafin Ramadan.

Kara karanta wannan
Yadda kisan Khamenei zai shafi 'yan Shi'a a Najeriya, rashinsa ya 'hada' kan Musulmi
Yan ta'addan sun kai hare-hare biyu a cikin dare guda, inda aka fara kai harin farko da 12.00 na tsakar dare tare da kashe mutum daya.
An kai hari na biyu ana sallar Asubahi, lamarin da ya jefa jama'a a cikin firgici bayan an kwashe wasu daga cikinsu zuwa dawa.
Asali: Legit.ng
