Tinubu Ya Tura Jakadun Najeriya Iran da Isra'ila yayin da ake tsaka da Gwabza Yaki
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura jakadu kasashen Iran da Isra'ila yayin da suke cigaba da fuskantar juna da hare hare a faden daga
- Mutanen da shugaban kasar ya tura na cikin jerin jakadu 63 da za su wakilci Najeriya a kasashe daban-daban bayan majalisa ta tantance su
- Fadar shugaban kasa ta ce Salau Mohammed zai wakilci Najeriya a Iran yayin da Nkechi Ufochukwu za ta tafi kasar Yahudawa ta Isra'ila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tura jakadun Najeriya zuwa Iran da Isra’ila a yayin da rikici da tashin hankali ke ƙaruwa a Gabas ta Tsakiya.
Tun a shekarar 2025 majalisar dattawa ta tantance mutane 63 da Shugaba Bola Tinubu ya amince a tura su kasashe su wakilci Najeriya.

Source: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa sunayen mutanen da Bola Tinubu ya tura Iran da Isra'ila a shafinsa na Facebook.
Jakadun Najeriya a Iran da Isra'ila
Fadar shugaban ƙasa ta sanar a ranar Juma’a cewa an tura Salau Mohammed zuwa Iran yayin da aka tura Nkechi Ufochukwu zuwa Isra’ila.
An tura su ne tare da wasu mutum 63 da aka aika zuwa wasu ƙasashe bayan majalisar Dattawa ta tantance su a watan Disamban 2025.
Naɗin su a matsayin jakadu ya zo kwanaki shida bayan da Amurka da Isra’ila suka kai wani hari kan Iran, lamarin da ya jawo babban rikici da tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.
Su wanene jakadun Najeriya a kasar Iran
Rahoton Premium Times ya nuna cewa tura jakadun da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ya zo ne shekaru uku bayan fara mulkinsa.
Salau Mohammed da aka tura Iran ƙwararren jami’in diflomasiyyar Najeriya ne daga Jihar Neja, kuma mamba ne na ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya.
A baya, Salau ya wakilci Najeriya a yankin Gulf, musamman a ƙasar Qatar, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labarai suka nuna.

Source: Twitter
Nkechi Ufochukwu da za ta tafi Isra'ila kuma ba kwararriya ba ce a fannin diflomasiyya; a baya ta yi aiki a matsayin mai ba ministan kimiyya da fasaha shawara a fannin shari’a.
Har yanzu ba a bayyana ko sababbin jakadun da aka naɗa zuwa Iran da Isra’ila za su tafi ƙasashen da za su yi aiki a ciki nan ba da daɗewa ba ko kuma ko yaƙin da ke tafiya zai iya hana tafiyarsu.
Maganar Jakadan Iran a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Jakadan Iran a Najeriya, Gholamreza Ahdavi Raja ya yi magana game da yakin da ake yi da kasar shi.
Gholamreza Ahdavi Raja ya bayyana cewa ba za su bar Donald Trump ya tsoma baki a kan zaben sabon jagora da za su yi ba.
Ya fadi haka ne bayan shugaban Amurka ya nuna cewa dole ne a saka shi a cikin masu tantance wanda zai zama sabon jagoran Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

