Mai Sa Ran Tagwaye Ta Haifi ’Yan 4, An Tsare Mai Jego a Asibiti Sai Ta Biya N3m

Mai Sa Ran Tagwaye Ta Haifi ’Yan 4, An Tsare Mai Jego a Asibiti Sai Ta Biya N3m

  • Abin al'ajabi ya faru bayan wata mata yar Najeriya mai shekaru 28, Charity Anani, ta ce ta haifi jarirai hudu lokaci guda
  • Iyalin sun shiga damuwa bayan asibiti ya bukaci su biya kudin jinya Naira miliyan uku, lamarin da ya sa har yanzu suna makale a asibitin
  • Matar ta ce jarirai hudu na raye, uku maza daya mace, duk da cewa biyu daga cikinsu sun samu matsalar lafiya bayan haihuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Calabar, Cross River - Wata mata mai shekaru 28 daga Cross River, Charity Anani, ta bayyana yadda ta yi mamakin ganin ta haifi jarirai hudu.

Matar ta ce ta yi tsammanin haihuwar jarirai biyu ne amma abin mamaki sai ga shi ta haifi har guda hudu kuma a lokaci guda.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu ta tara mata Musulmi da Kirista a azumi, ta ja kunne kan bude tsiraici

Mata ta haifi jarirai 4 bayan tsammanin guda 2
Mata mai shekaru 38 ta jera jarirai 4 da ta haifa. Hoto: Ahmed Zakot/SOPA Images/LightRocket.
Source: Getty Images

Mata ta haifi jarirai 4 bayan tsammanin 2

Anani ta ce binciken da ta yi a lokacin daukar ciki ya nuna jarirai biyu ne kawai, amma a lokacin haihuwa sai aka gano cewa har yanzu akwai wasu biyu a cikinta, cewar Punch.

Ta bayyana cewa ta haifi jarirai biyu da kanta, kafin likita ya lura cewa akwai sauran jarirai biyu a cikinta, wannan ya kara ba ta mamaki sosai.

Mijinta wanda ke aikin tuka babur na haya ya ce ya yi matukar mamaki da farin ciki tare da damuwa saboda halin kuncin tattalin arziki.

Matar ta yi korafin miliyoyin kudin jinya

Anani ta ce jariran da ta haifa uku maza ne daya mace, kuma an haife su ne a ranar 27 ga Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.

Ta bayyana cewa ko da yake an sallame ta daga asibiti, amma kudin jinya na kusan Naira miliyan uku ya hana su komawa gida.

Kara karanta wannan

Malamai a siyasa: Sheikh Abdulmuddalib zai nemi gwamnan Zamfara a 2027

Ta kara da cewa jarirai biyu na karshe sun ji rauni bayan haihuwa, inda ake ba su kowane tulun iskar 'oxygen' kan kudi N55, 000.

An rike mata a asibiti bayan ta haifi jarirai 4
Taswirar jihar Cross River da wata mata ta haifi jarirai 4. Hoto: Legit.
Source: Original

Halin da jariri 1 ke ciki a asibiti

Sannan ta ce jaririn karshe yana cikin na’ura wanda ake biyan N50, 000 a kowace rana domin kula da lafiyarsa wanda hakan yake neman zama matsala ga iyalansu.

Matar ta ce duk da wahalar daukar cikin jarirai hudu, tana godiya ga Allah saboda ta haife su lafiya kuma dukkan su na raye.

Ta kara da cewa ita da mijinta suna fatan samun taimakon jama’a domin su iya biyan kudin asibiti da kuma kula da jariran da Allah ya azurta su da su.

An yi martani bayan mata ta haifi jarirai 4

A baya, an ji cewa wata mata da ke da tsarin haihuwar yaro daya ta bayyana kaduwa lokacin da ta samu juna biyun jarirai hudu lamarin da ya jawo magana a kafofin sadarwa.

Bayan ta haifi yaran, ta dora su a kan kujera yayin da mutane da yawa a TikTok suka yaba da kyawunsu yayin da wasu suka yi martani da dama.

Wasu masu amfani da kafar sada zumunta sun yi kokarin bayyana mata tasiri da kuma amfanin jariran nata amma wasu ko na yi mata gargadi kan kula da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.