Kyauta daga Allah: Wata mata ta haifi ‘yan 4 a Sokoto

Kyauta daga Allah: Wata mata ta haifi ‘yan 4 a Sokoto

- Wata mace da Allah ya yiwa baiwar haihuwan ‘yan hudu a jihar Sokoto ta ja hankalin mutane a intanet

- Matar da jaririran na cikin koshin lafiya

Wata mata ta haifi ‘yan 4 a Sokoto
Wata mata ta haifi ‘yan 4 a Sokoto

Allah ya azurta wata mace da haihuwar ‘yan hudu a jihar Sakkwato

Matar wacce aka ya sa labarinta a shafin sada zumunta da muhawara na Facebook ta sha Barka da jinjina daga ‘yan Najeriya wadanda suka karanta labarin ba tare da banbancin addini ko yare ba.

Wanda hakan ya gaskanta karin maganar bahaushe da ke cewa, da na kowa ne, ballanta jarirai sabbin haihuwa na ban mamaki irin wannan.

Matar wacce ba a bayyana sunan ta ba, ko na namijinta, kamar yadda labarin ya nuna, ta haihu ne a ranar Laraba 22 ga watan Disamba shekarar 2016 a wata unguwa maui suna ‘Abdallah’ kamar yadda aka labarta.

KU KARANTA KUMA: An yi ma barayin Bunsuru horo mai tsanani a kasar Kenya

Ba a dai bayyana sunan matar ba illa dai cewa a garin Sakkwato matar ta haihu kuma ita jaririran nata hudu, na cikin koshin lafiya a asibiti.

Sai dai ba kamar yadda wasu ke shiga halin ni ‘ya su da kuma damuwa ba da zaran sun samu karuwa musamman a lokacin matsi irin wannan, Mai jegon kamar yadda hoton ya nuna na fara’a, babu kuma ko alamar damuwa a tattare da ita.

Mu ma a nan Legit.ng mu na yi mata fatan Alheri, tare da addu’ar Allah Ya raya 'yan hudu, Ya sa kuma zu zama nagari da kasa za ta amfana.

Ku cigaba da biyo mu tare da bayyana ra'ayinku kan wanna labari a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: