Amurka Ta Shiga Uku, Shugaban Rasha, Putin Ya Kira Shugaban Iran Ta Wayar Tarho
- Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya tattauna da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian ta wayar tarho yau Juma'a
- Bayanai sun nuna cewa shugabanin biyu sunn tattauna kan batutuwan da suka shafi yakin da ya barke tsaka Amurka, Isra'ila da Iran
- Vladimir Putin ya mika sakon ta'aziyya ga daukacin al'ummar Iraniyawa kan rasuwar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, sun yi wata tattaunawa ta wayar tarho yayin da musayar wuta ke kara kamari a Gabas ta Tsakiya.
Rahoto ya nuna cewa Shugaba Putin da takwaransa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun tattauna kan yaƙin da ya barke tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran.

Source: Getty Images
Vladimir Putin ya yi magana da Shugaban Iran
RBC Ukraine ta tattaro cewa wannan tattaunawa tsakanin shugabannin biyu na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara rade-radin cewa Rasha na tallafawa Iran a yakinta da Amurka

Kara karanta wannan
Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran
An ruwaito cewa shugaban Iran ya gode wa Putin bisa abin da ya kira goyon bayan Rasha ga al’ummar Iran, tare da ba shi bayani kan yadda rikicin ke tafiya.
A nasa bangaren, Putin ya jaddada bukatar kawo karshen faɗa a Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa ya kamata a koma kan hanyar tattaunawa da diflomasiyya domin warware matsalar.
Putin ya yi ta’aziyyar rasuwar Khamenei
Shugaba Putin ya kuma mika ta’aziyyarsa kan kashe tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya rasu a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.
Har ila yau, shugaban na Rasha ya yi alhini kan mutuwar fararen hula da dama da ya danganta da hare-haren a “Amurka da Isra’ila kan Iran.”
Rahotanni sun ce shugabannin biyu sun amince da ci gaba da tuntubar juna ta hanyoyi daban-daban yayin da rikicin ke ci gaba.
Jita-jitar taimakon soja daga Rasha
A baya dai Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi ishara cewa hadin gwiwar da ke tsakanin Iran da Rasha na ci gaba da aiki, duk da yaƙin da Iran ke yi da Amurka da Isra’ila.

Source: Getty Images
Jaridar The Washington Post ta kuma ruwaito cewa akwai yiwuwar Moscow na ba Tehran bayanan sirri kan wuraren sansanonin sojojin Amurka.
Rahoton ya ce daidaiton hare-haren da Iran ke kai wa wuraren Amurka na iya zama hujjar cewa tana samun irin wannan taimako
Trump ya sa sharadin daina yaki da Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya bayyana cewa mika wuyan Iran ba tare da sharadi ba ne kadai zai kawo karshen yakin da ya barke.
Wannan furuci na Trump ya zo ne a lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan wuraren gwamnati a birnin Tehran na Iran.
Trump ya ƙara da cewa idan Iran ta amince da wannan sharadi na mika wuya, Amurka da ƙawayenta za su taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
