Cikakken Jerin Sunaye da Kasashen da Tinubu Ya Tura Sababbin Jakadun Najeriya

Cikakken Jerin Sunaye da Kasashen da Tinubu Ya Tura Sababbin Jakadun Najeriya

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da tura jakadu 65 wadanda aka nada zuwa kasashe daban-daban da kuma Majalisar Dinkin Duniya (UN) domin karfafa wakilcin Najeriya a kasashen waje.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ne ya sanar da wannan mataki a ranar Alhamis, 6 ga watan Maris 2026.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da tura sababbin jakadun Najeriya zuwa kasashe daban daban
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na rattaba hannu kan wata takarda a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Bola Tinubu ya tura jakadu zuwa kasashen waje

A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Onanuga ya ce jerin sunayen ya kunshi mutane 31 da ba ma'aikatan diflomasiyya ba (non-career) da kuma kwararrun ma'aikatan diflomasiyya (career diplomats) guda 34.

A cikin watan Nuwamban shekarar da ta gaba ne Shugaba Tinubu ya zaɓi waɗannan mutane, inda daga bisani Majalisar Dattawa ta tantance su tare da tabbatar da naɗin nasu a watan Disamba.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar tsohon ministan Tinubu ya yake shi, yana kus kus da kusoshin adawa

Ma'aikatar harkokin waje ta riga ta karɓi amincewar ƙasashe irin su Birtaniya don tura Jakada Aminu Dalhatu, da kuma ƙasar Faransa don tura Jakada Ayo Oke.

1. Jerin jakadu 31 (Non-Career)

Wannan rukunin ya ƙunshi fitattun ƴan siyasa da tsofaffin jami'an gwamnati:

S/N

Sunan jakada

Ƙasar da aka tura shi/ta

1

Grace Bent

Lome, Togo

2

Ita Enang

South Africa

3

Ikpeazu Victor

Spain

4

Nkechi Linda Ufochukwu

Tel-Aviv, Israel

5

Mahmood Yakubu

Qatar

6

Paul Oga Adikwu

Vatican City (Holy See)

7

Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas

Philippines

8

Reno Omokri

Mexico City, Mexico

9

Abasi Ebraimah

Budapest, Hungary

10

Erelu Angela Adebayo

Portugal

11

Olumilua Oluwayimika Ayotunwa

Tokyo, Japan

12

Ugwuanyi Ifeanyi Lawrence

Athens, Greece

13

Chioma Priscilla Ohakim

Poland

14

Aminu Dalhatu

United Kingdom

15

Abdulrahman Bello Dambazau

Beijing, China

16

Tasiu Musa Maigari

Gambia

17

Olufemi Pedro

Australia

18

Muhammed Ubandoma Aliyu

Argentina

19

Lateef Kayode Are

United States of America

20

Joseph Sola Iji

Russia

21

Jimoh Ibrahim

UN Permanent Representative

22

Femi Fani-Kayode

Germany

23

Prof. Isaak Folorunsho Adewole

Ottawa, Canada

24

Fatima Florence Ajimobi

Austria

25

Lola Akande

Sweden

26

Ayodele Oke

France

27

Yakubu Gambo

Saudi Arabia

28

Prof. Nora Ladi Daduut

Seoul, South Korea

29

Onueze Chukwujika Okocha

Dublin, Ireland

30

Kulu Haruna Abubakar

Tunis, Tunisia

31

Jerry Samuel Manwe

Port of Spain, T&T

Kara karanta wannan

Malamai sun yi magana, sun fadi yadda yakin Iran da Amurka ya shafi Najeriya

2. Ƙwararrun ma'aikatan diflomasiyya

Ga jerin kwararrun ma'aikatan diflomasiyya 34 da aka tura su kasashe daban daban:

S/N

Sunan jakada

Ƙasar da aka tura shi/ta

1

Nwabiola Ezenwa Chukuwemeka

Cote D'Ivoire

2

Besto Maimuna Ibrahim

Niger

3

Monica Okwuchukwu Enebechi

Sao Tome, STP

4

Mohammed Mahmud Lele

Algiers, Algeria

5

Endoni Synoph Paebi

Ouagadougou, Burkina Faso

6

Ahmed Mohammed Monguno

Cairo, Egypt

7

Jane Adams

Kingston, Jamaica

8

Clark-Omeru Alexandra

Lusaka, Zambia

9

Chima Geoggrey David

Bamako, Mali

10

Odumah Yvonne Ehinosen

Malabo, E/Guinea

11

Wasa Segun Ige

Beirut, Lebanon

12

Ruben Abimbola Samuel

Rome, Italy

13

Onaga Ogechukwu Kingsley

Maputo, Mozambique

14

Magaji Umar

Kinshasa, DR Congo

15

Muhammed Saidu Dahiru

New Delhi, India

16

Abdulssalam Habu Zayyad

Dakar, Senegal

17

Shehu Ilu Barde

Accra, Ghana

18

Aminu Nasir

Ethiopia

19

Abubakar Musa Musa

N'Djamena, Chad

20

Haidara Mohammed Idris

The Hague, Netherlands

21

Bako Adamu Umar

Rabat, Morocco

22

Sulu-Gambari Olatunji Ahmed

Malaysia

23

Romata Mohammed Omobolanle

Tanzania

24

Shaga John Shamah

Botswana

25

Salau Hamza Mohammed

Tehran, Iran

26

Ibrahim Danlami

Kenya

27

Ibrahim Adeola Mopelola

Cotonou, Benin

28

Ayeni Adebayo Emmanuel

Brussels, Belgium

29

Akande Eahab Adekola

Berne, Switzerland

30

Arewa Esther

Windhoek, Namibia

31

Gergadi Joseph John

Libreville, Gabon

32

Luther Ogbomode Ayo-Kalata

Sierra-Leone

33

Danladi Yakubu Nyaku

Khartoum, Sudan

34

Bello Dogon-Daji Haliru

Bangkok, Thailand

Kara karanta wannan

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Muhimman abubuwan da suka faru a rana ta 5

Shugaba Tinubu ya ba ma'aikatar harkokin waje umarnin fara gudanar da taron bita ga sababbin jakadun cikin gaggawa.

Wannan naɗi ya zo ne bayan da masu sukar gwamnati suka koka kan cewa rashin jakadu na haifar da giɓi a wakilcin Najeriya a idon duniya.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Jakadu da Tinubu ya naɗa sun shiga matsala

A wani rahoto, mun ruwaito cewa, wasu ƙasashe na iya ƙin karɓar jakadun shugaban Najeriya, Bola Tinubu saboda ƙarancin lokacin wa’adin mulkinsa.

A halin yanzu, ma’aikatar harkokin waje na fama da samun yarjejeniyar karbar jakadun yayin da zaɓen 2027 ke gabatowa, abin da ke sa ƙasashen waje nuna jinkiri.

Tun da ma can, masana diflomasiyya sun ce jinkirin nadin jakadu kuskure ne, kuma hakan na iya rage tasirin Najeriya a hulɗar ƙasa da ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com