'Yan Bindiga Sun Kashe Mahaifin Tsohon Mataimakin Gwamna a Najeriya
- 'Yan bindiga sun yi aika-aika bayan sace wani basarake a jihar Ebonyi da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
- Tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken ne wanda ya kasance mahaifin tsohon gwamnan jihar zuwa cikin daji
- Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta karin haske kan kokarin da ta yi wajen ceto basaraken wanda daga 'yan bindigan suka kashe
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ebonyi - 'Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe basaraken garin Ndufu-Alike da ke ƙaramar hukumar Ikwo a jihar Ebonyi, Ezeogo Francis Igwe, wanda suka yi awon gaba da shi a baya.
Ezeogo Francis Igwe, wanda shi ne mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar, Kelechi Igwe, an yi garkuwa da shi ne ranar Lahadi, 1 ga watan Maris, 2026, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa coci a garin Ndufu-Alike.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta ce Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ebonyi, Joshua Ukandu, ya bayyana cewa an kashe basaraken ne kwana ɗaya bayan an yi garkuwa da shi.
'Yan sanda sun yi kokacin ceto shi
Joshua Ukandu ya bayyana cewa bayan sace basaraken, jami’an rundunar sun ƙaddamar da gagarumin aikin ceto domin kubutar da shi.
“Bayan sace Eze Francis Igwe a ranar 1 ga Maris, 2026, nan ta ke jami’an rundunar jihar Ebonyi suka fara gagarumin aiki da nufin ceto basaraken."
- Joshua Ukandu
An cafke wadanda ake zargi da laifi
Kakakin rundunar ya ƙara da cewa ta hanyar amfani da dabarun fasaha da tattara bayanan sirri, jami’ai sun kama mutane biyu da ake zargin mambobin ƙungiyar masu garkuwar ne da suka aikata laifin.
Ya ce yayin gudanar da bincike, waɗanda ake zargin sun amsa cewa an kashe basaraken ne a ranar 2 ga watan Maris, 2026, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
Wadansa ake zargin sun kuma amince su jagoranci jami’an tsaro zuwa maboyarsu domin kwaso gawar mamacin.
Joshua Ukandu ya ci gaba da bayyana cewa lokacin da jami’an ’yan sanda suka kusanci maboyar, sauran mambobin ƙungiyar sun buɗe musu wuta, wanda hakan ya janyo artabu tsakaninsu.
“Sai dai bayan kusantar maboyar, sauran mambobin ƙungiyar sun buɗe wa jami’ai wuta. Jami’an sun mayar da martani da wuta mai zafi wadda ta fi ƙarfin 'yan ƙungiyar."
- Joshua Ukandu

Source: Original
An kashe dan bindiga yayin artabu
’Yan sandan sun ƙara da cewa an kashe ɗaya daga cikin maharan yayin artabun, yayin da sauran suka tsere daga wurin.
Bayan haka, jami’an ’yan sanda sun kama ƙarin wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a laifin, sannan sun gano bindiga ɗaya ƙirar gida a hannunsu.
Ya ce waɗanda ake zargin suna tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere.
'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan jami'an 'yan sanda a jihar Kebbi.
'Yan bindigan sun kashe 'yan sanda biyu yayin wani hari da suka kai kan shingen binciken ababen hawa a karamar hukumar Bagudu ta jihar Kebbi.
Maharan sun far wa shingen ’yan sandan ne da ke kan hanyar kan iyaka ta Bakin Ruwa zuwa Maje, inda suka buɗe wa jami’an da ke gadin wurin wuta.
Asali: Legit.ng


