Tofa: Isra'ila Ta Fadawa Tinubu Kasar da ke Daukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya

Tofa: Isra'ila Ta Fadawa Tinubu Kasar da ke Daukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya

  • Jakadan Isra'ila Michael Freeman ya zargi kasar Iran da daukar nauyin ta'addanci a Najeriya da kasashen yankin Afirka ta Yamma
  • Freeman ya bayyana cewa Isra'ila tana da hakki na kare kanta daga barazanar makaman nukiliya da manufofin kisan kiyashi na Iran
  • Jakadan ya ce Isra'ila a shirye take ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta'addanci da kuma dukkan ayyukan rashin zaman lafiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jakadan Isra'ila, Michael Freeman, ya fadawa gwamnatin Bola Tinubu kasar da suke zargin take daukar nauyin ta'addanci Najeriya.

Freeman ya yi ikirarin cewa Iran ce take rura wutar ta'addanci a Najeriya tare da goyon bayan ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, don dagula zaman lafiyar Afirka ta Yamma.

Isra'ila ta yi ikirarin cewa Iran na daga cikin masu daukar nauyin ayyukan ta'addanci a Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu (hagu), Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi (tsakiya) da jakadan Isra'ila a Najeriya, Michael Freeman (dama). Hoto: @officialABAT, @M_S_Freeman/X da AFP via Getty Images
Source: Twitter

Masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise News yau Juma'a, Freeman ya bayyana cewa an daɗe ana samun rahotanni kan ayyukan ta'addancin Iran a sassa daban-daban na duniya, kuma yanzu ayyukansu sun mamaye ƙasashen Afirka, ciki har da Najeriya.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, harin Hezbollah ya rutsa da dan babban Minista a Isra'ila

Jakadan ya ambaci ƙungiyar mabiya Shi'a ta Najeriya (IMN) a matsayin ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da gwamnatin Iran ke ɗaukar nauyin ayyukansu.

Freeman ya ce wannan ba ikirari ne daga gare shi ba kawai, domin har tsohon jagoran Iran, Ayatollah Khomeini, ya taɓa wallafa goyon bayansa ga ƙungiyar a dandalin X.

Jakadan ya bayyana cewa Iran ba Najeriya kaɗai take ƙoƙarin dagula wa lissafi ba, har ma da daukacin yankin Afirka ta Yamma.

Isra'ila ta zargi Iran da mallakar nukiliya

Freeman ya kare matakin da Isra'ila ta ɗauka na kai hari kan Iran, inda ya bayyana hakan a matsayin matakin kariya ga ƙasarsa sakamakon manufofin Iran na tsawon shekaru 47.

Ya jaddada cewa Iran ita ce ƙasa ɗaya tilo a duniya dake da manufar goge wata ƙasa daga doron ƙasa, kuma tana ci gaba da haɓaka shirinta na makaman nukiliya da makaman linzami.

Lokacin da aka tambaye shi game da makaman nukiliya na Isra'ila, Freeman ya bayyana cewa kasarsa ba ta taɓa cewa tana da su ba, kuma ba ta fatan kasancewa ƙasar farko da za ta fara amfani da makaman nukiliya a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun sace daruruwan mutane bayan kai hari a Borno

"Babbar matsalar a nan ita ce Iran. Iran ita ce kadai kasar duniya a Majalisar Dinkin Duniya, wacce ta fito karara ta nuna kudurinta na shafe wata kasa daga doron duniya. Iran ta ce burinta shi ne tarwatsa Isra'ila, shafe Isra'ila daga doron duniya, a kashe duk wani abu da ke numfashi."

- Michael Freeman.

Isra'ila ta ce a shirye take da taimaka wa Najeriya don yaki da dukkan matsalolin tsaro a kasar.
Jakadan Isra'ila a Najeriya, Michael Freeman yana jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: @M_S_Freeman
Source: Twitter

Isra'ila ta shirya taimakawa Najeriya

Jakadan ya jaddada cewa Najeriya da Isra'ila ƙawayen juna ne tun tale-tale, kuma ƙasarsa a shirye take ta taimaka wa Najeriya wajen shawo kan matsalolin tsaro.

Ya ambato kalaman Firayiminista Benjamin Netanyahu na cewa Isra'ila tana sha'awar yin haɗin gwiwa da Najeriya bisa buƙatun ƙasar domin yaƙar duk wani nau'i na rashin zaman lafiya.

Freeman ya lissafo hare-haren ta'addanci da Iran ta kai a sassa daban-daban kamar Turai, Argentina, Bulgaria, da kuma cikin Afirka, inda ya ce dukkan waɗannan ayyuka na da nufin cimma burin Iran na ruguza Isra'ila.

"Mun ga yadda suke gudanar da ayyukansu a Najeriya. Mun ga yadda mutanen nan suke wanzar da rashin zaman lafiya a kasashen duniya, kuma duk dai manufarsu ita ce tarwatsa Isra'ila."

- Michael Freeman.

'Yan Shi'a sun yi zanga-zangar kisan Khamenei

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan kungiyar IMN, wadda aka fi sani da ‘yan Shi’a, karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, sun gudanar da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Bayan Amurka ta dora mata laifi, Isra'ila ta fadi dalilin kashe Ayatollah Khamenei

Sun yi zanga-zangar ne a jihohin Gombe, Neja, Kano, Bauchi, Yobe da Sakkwato kan kisan Jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Rahotanni sun bayyana cewa zanga-zangar ta biyo bayan wani harin sama da aka ce hadin gwiwar Amurka da Isra’ila ne suka kai a Iran, wanda ya janyo mutuwar Khamenei.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com