Ana tsaka da Yakin Iran, Isra’ila, an Bankado Asirin Trump a Badakalar Esptein

Ana tsaka da Yakin Iran, Isra’ila, an Bankado Asirin Trump a Badakalar Esptein

  • Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta fitar da sababbin takardun binciken hukumar FBI da ke kunshe da zarge-zarge kan Donald Trump
  • Takardun sun bayyana cewa wata mata ta zargi Trump da Jeffrey Epstein da cin zarafinta lokacin da take tsakanin shekaru 13 zuwa 15
  • Trump ya musanta zargin da ake yi masa, yayin da ‘yan jam’iyyar Democrat ke zargin gwamnatin sa da boye wasu bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta fitar da sababbin takardun binciken Hukumar FBI game da zarge-zarge kan Donald Trump.

Takardun Jeffrey Epstein da aka samu sun shafi zarge-zargen cin zarafin wata mata da ake dangantawa da Trump wanda tuntuni ya karyata zargin da ake yi masa.

An bankado wani sirrin Trump a takardun Epstein
Shugaba Donald Trump na Amurka yayin jawabi a Washington. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

Epstein: An fitar da takardun Donald Trump

Takardun sun bayyana bayanan hirarraki da jami’an FBI suka yi a shekarar 2019 da wata mata da ta ce an gabatar da ita ga Trump ta hannun Epstein, cewar Sky News.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya

A cewar matar, an kai ta ko dai New York ko New Jersey inda Epstein ya gabatar da ita ga Trump kafin daga baya a ce ya yi kokarin tilasta mata yin lalata.

Ta ce ta ciji Trump yayin da yake kokarin tilasta mata yin lalata da ita ta bakinta, kuma ta sha samun kiran barazana daga wasu mutane su na bukatar ta yi shiru.

Ma’aikatar shari’a ta ce takardun ba a fitar da su a baya ba saboda an yi musu alamar cewa sun maimaitu a cikin bayanan da aka saki.

Trump ya musanta duk wani laifi da ake danganta masa da zargin Epstein, yana mai cewa wasu daga cikin takardun na dauke da labaran karya.

Sai dai ‘yan jam’iyyar Democrat sun zargi gwamnatin Trump da kokarin boye wasu bayanai da ka iya jawo masa matsala a siyasa, cewar rahoton Al Jazeera.

An bankado wasu bayanai kan Trump daga takardun Epstein
Marigayin dan kasuwa, Jeffrey Epstein da Donald Trump a tsibirin Palm da ke Florida. Hoto: Davidoff Studios.
Source: Getty Images

Ana zargin Trump na neman kawar da hankula

A ranar Laraba 4 ga watan Maris, 2026 kuma, wani kwamitin majalisar wakilan Amurka ya kada kuri’ar neman tilasta wa ministar shari’a Pam Bondi amsa tambayoyi kan batun takardun Epstein.

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi, Trump ya ja da baya, ya ki tura sojoji Iran

Wani dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican a Amurka, Thomas Massie ya taimaka wajen ganin an amince da dokar takardun Epstein.

Massie a bara, ya ce, “jefa bama-bamai kan wata kasa da ke wani bangare na duniya ba zai sa takardun Epstein su bace ba”.

Shaiel Ben-Ephraim, mai sharhi a cibiyar 'Atlas Global Strategies' kuma tsohon jami’in diflomasiyyar Isra’ila, ya shaida cewa Trump “yana matukar bukatar wani abu da zai dauke hankalin jama’a daga matsalolinsa na cikin gida, kamar yaki”.

An bankado alakar Epstein, Isra'ila da Boko Haram

An ji cewa sabon bincike ya danganta marigayi Jeffrey Epstein da tsohon Firaministan Isra’ila, Ehud Barak da Boko Haram da ta addabi yankin Arewa maso Gabas a Najeriya.

Rahoton ya ce an yi amfani da tattaunawar tashoshin jiragen ruwa a Lagos da Badagry, da kuma fasahar tsaro, domin samun moriyar kasuwanci a Najeriya.

Binciken ya yi zargin cewa hanyoyin tsaro da jarin da aka zuba sun ba bangarorin damar cin gajiyar rashin zaman lafiyar da ke faruwa wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.