Matar Tinubu Ta Tara Mata Musulmi da Kirista a Azumi, Ta Ja Kunne kan Bude Tsiraici

Matar Tinubu Ta Tara Mata Musulmi da Kirista a Azumi, Ta Ja Kunne kan Bude Tsiraici

  • Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi magana kai tsaye ga mata da suke bude jikinsu a matsayin ado
  • Oluremi ta bukaci mata su riƙa ɗaukar nauyin ƙananan ’yan mata domin koya musu tarbiyya, mutunci da darajar rayuwa a Najeriya
  • Ta yi wannan kira ne a wani taron buda baki na Musulmi da na Kirista da ta shirya a Abuja, inda ta jaddada muhimmancin ba ’yan mata ilimi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta halarci taron buda baki da aka shirya ga mata Musulmi da Kirista a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Oluremi ta bukaci mata a fadin Najeriya su rika daukar nauyin ’yan mata kanana domin koya musu tarbiyya, mutunci da dabarun rayuwa mai kyau.

Oluremi Tinubu ya shawarci mata kan shiga mai kyau
Matar shugaban kasar Najeriya, Oluremi Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Sen. Oluremi Tinubu.
Source: Facebook

Ta yi wannan magana ne yayin wani taron buda baki na Musulmi da Kirista da ta shirya a Abuja ranar Alhamis, 5 ga Maris, 2026 da @emmaikumeh ya wallafa bidiyon a X.

Kara karanta wannan

Malamai sun nuna kishi, sun goyi bayan 'dan APC domin samun Musulmin gwamna

Kalubalen da Oluremi Tinubu ta tura ga mata

A jawabinta, ta kalubalanci mata su daukar akalla yarinya daya daga al’umma marasa karfi domin ba ta shawara, tallafi ko ma gurbin karatu.

Ta ce:

“Ina kalubalantar ku, ku rika daukar yara mata. Ku ba da gudunmawa a rayuwar wata yarinya daga al’ummomi ko marasa karfi domin taimaka mata.”

Uwargidan shugaban kasar ta kuma bukaci mata su koyar da ’yan mata dabi’u nagari, yadda za su zama mata na gari da kuma yadda za su rika sanya tufafi masu kamala.

Ta kara da cewa ya kamata ’yan mata su rika rufe jikinsu yadda ya dace, tana mai nuna damuwa kan yadda wasu ke sanya tufafi marasa kamala.

Matar Tinubu ta tura roko ga mata kan kamala
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu tana jawabi ga mata a Abuja. Hoto: Sen. Oluremi Tinubu.
Source: Facebook

Oluremi Tinubu ta ja kunne kan ado, tsiraici

A cewarta, kyawu na gaskiya ba ya fitowa daga nuna tsiraici, sai dai daga dabi’a mai kyau da halaye nagari da ke cikin mutum wanda zai taimaka masa a rayuwa.

Ta ce:

“Nuna tsiraici ba ado ba ne. Ba mu san dalilin da ya sa suke yin haka ba, amma kyawu na gaskiya yana fitowa daga zuciya.”

Kara karanta wannan

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Muhimman abubuwan da suka faru a rana ta 5

Oluremi Tinubu ta kuma jaddada cewa maza ma suna da rawar takawa wajen karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma.

Ta ce tana fatan Allah zai taimaki maza su rika kula da halayensu da kuma yadda suke kallon mata a cikin al’umma ba tared da nuna wariya ko cin zarafi ba, cewar TheCable.

Oluremi Tinubu ta magantu kan kalubalen auren Musulmi

A baya, an ji cewa Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta yi magana game da kalubale da ta fuskanta bayan auren Bola Tinubu a Najeriya.

Oluremi ta ce ta taba fuskantar tsangwama saboda aurenta da Musulmi, tana mai karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya duba da yadda lamarin ya tayar da jijiyoyin wuya.

Ta bayyana haka ne a wata hira da ta aka tambaye ta game da zargin kisan Kiristoci inda ta ce ta'adanci ya shafi kowa a kasar ba tare da bambance mutum Kirista ne ko Musulmi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.