Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Ma'aikata Gata, Ta Fito da Sabon Tsarin da Zai Amfane Su bayan Ritaya
- Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta cimma matsaya kan sabon tsarin giratuti wanda zai amfani ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka gama aiki
- Sabon tsarin giratutin zai amfani ma'aikatan da suka yi aiki da gwamnatin tarayya akalla na shekarar 10 damar samun kaso 100 cikin 100 na albashinsu
- Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Didi Esther Wilson-Jack ta yabawa majalisar zartarwar kan amincewa da sabon tsarin wanda zai amfani ma'aikata
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da wani sabon tsarin giratuti ga ma'aikatan gwamnatin tarayya.
Sabon tsarin da Majalisar zartarwar ta amince da shi zai ba ma'aikatan gwamnatin tarayya damar samun garatuti da ya yi daidai da kashi 100 cikin 100 na jimillar albashinsu na shekara guda.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya ya fitar a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2026. a Abuja.

Kara karanta wannan
Iran ta harba makamai masu linzami kan babban birnin Isra'ila, an ji barnar da suka yi
Wan tsarin giratuti gwamnati ta fito da shi?
Sabon tsarin biyan kudin giratutin dai zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Janairun 2026, labarin ya zo a jaridar The Punch.
A ƙarƙashin wannan tsari, ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka yi aiki na aƙalla shekaru 10 za su karɓi giratuti idan sun yi ritaya, baya ga sauran alfanun da suke samu a ƙarƙashin tsarin fansho da ake kai yanzu.
An tattauna sosai kan sabon tsarin giratuti
Bisa ga sanarwar, amincewar ta biyo bayan tattaunawa mai zurfi da kuma shawarwarin daga wani kwamiti na ministoci da ofishin shugabar ma'aikata ta tarayya ya kafa.
Kwamitin ya yi aiki tare da hukumar kula da fansho ta kasa, ofishin kasafin kuɗi na tarayya, da kuma ofishin akanta-janar na tarayya domin samar da abin da suka bayyana a matsayin tsari mai dorewa na aiwatar da wannan shiri.
Shugabar ma'aikata ta yabawa gwamnatin tarayya
Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Didi Esther Walson-Jack ta jinjina wa majalisar saboda amincewa da wannan shiri, inda ta bayyana shi a matsayin babban mataki na inganta jin daɗin ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan
"Kada a dagula siyasar Kano": NNPP ta aika sako kan shirin tsige Mataimakin gwamna

Source: Facebook
Ta ce wannan shawara ta nuna cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana daraja jajircewa da sadaukarwar ma'aikatan gwamnati.
"Wannan amincewa wata babbar shaida ce ta karrama gudunmawar da ma'aikatanmu suka bayar, waɗanda suka sadaukar da mafi kyawun lokutan rayuwarsu wajen yi wa ƙasa hidima da kuma ci gaban ƙasa."
- Didi Esther Walson-Jack
Gwamnatin tarayya ta gano masu fama da talauci
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta kara zage damtse a kokarin da take yi na yakar talauci a Najeriya.
Gwamnatin ta yi ikirarin cewa zuwa yanzu, ta kammala gano mutanen da suka fi ko wadanne fama da talauci da kuncin rayuwa.
Ministan harkokin jin kai, Dr. Benard Doro ya bayyana cewa gwamnatin Tarayya ta yi nasarar gano gidaje mafi talauci a Najeriya ta hanyar rijistar jin-ƙai ta ma’aikatarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng