'Yajuju da Majuju Sun Bayyana Suna Kashe Mutane a Duniya,' Sheikh Gumi

'Yajuju da Majuju Sun Bayyana Suna Kashe Mutane a Duniya,' Sheikh Gumi

  • Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa Yajuju da Majuju sun riga sun bayyana a duniyar yau
  • Rahoto ya nuna cewa malamin ya yi magana ne yayin gabatar da tafsirin Ramadan a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2026 a jihar Kaduna
  • Sheikh Gumi ya yi magana ne yayin da ake cigaba da kashe-kashe a duniya, musamman bayan barkewar yakin Amurka da kasar Iran

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa a yanzu haka Yajuju da Majuju sun bayyana a duniya.

A bayanin da ya yi, babban malamin ya ce dama asali Yajuju da Majuju cikin dan Adam suke kawai kabilarsu ce ta bambanta da ta sauran jama'a.

Kara karanta wannan

Komai ya fito: An fadi aikin da sojojin Amurka da aka jibge a Bauchi za su yi

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi a wani taro. Hoto: Salisu Hassan
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa malamai ya fadi haka ne a majalisin tafsirin da ya ke a jihar Kaduna kamar yadda bidiyon da ya wallafa a Facebook ya nuna haka.

Su wane ne Yajuju da Majuju?

Sheikh Gumi ya bayyana cewa akwai wani babban malami Balarabe, Muhammad Al-Idrisi da ya fara samar da taswirar duniya, wanda Turawa suka nemi ya musu a lokacin.

A taswirar da Balaraben ya yi, Sheikh Gumi ya ce an bayyana garin da Yajuju da Majuju da za su fito, inda ya ce:

"Mutane ne kamar mu,"

A kan haka ya karyata labarin da ake cewa Yajuju da Majuju wasu halittu ne masu manyan kunnuwa da har za su iya bargo da su.

Shafin kundin tattara bayanai na Britanica ya nuna cewa Muhammad Al-Idrisi ya yi aiki da Turawa sosai wajen tsara taswirar duniya.

Yajuju da Majuju sun fito inji Gumi

Kara karanta wannan

Malamai a siyasa: Sheikh Abdulmuddalib zai nemi gwamnan Zamfara a 2027

A karkashin bidiyon da ya wallafa, malamin ya wallafa cewa Yajuju da Majuju sun bayyana kuma su ne ke barna a ko ina a yanzu.

A bayanin da ya yi, malamin ya ce:

"Tabbas wani a cikin mu ne Yajuju da Majuju"

Sheikh Gumi ya kara da cewa Kur'ani ya ce Yajuju da Majuju za su mamaye kowane tsibiri da bagare na duniya, sai ya yi tambaye da:

"Su waye suke kowane tsibiri na duniya a yau?"

Karin bayani kan Yajuju da Majuju

A karin bayani da ya yi, Sheikh Gumi ya ce Hadisi ya nuna cewa Yajuju da Majuju za su rika harba mashi sama suna kashe mutane.

Ya ce daga baya, idan sun gama da mutanen duniya za su fara harba makamai sama, a kan haka ya ce a 1945 bayan yakin duniya Turawa suka mamaye duniya.

Gumi ya ce a 1957 Rasha ta fara harba kumbo sama kafin daga baya Amurka ta bi bayan su, sai daga baya aka fara harba mutane duniyar wata a shekarun1960.

Shwikh Gumi ya yi wa Amurka raddi

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: Jiragen yakin Amurka sun ruguzo daga sama a Kuwait

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubaka Gumi ya bayyana cewa rayuwa karkashin dokokin Shari'ar Musulunci hakkin Musulmi ne.

Ya fadi haka a matsayin martani ga wasu 'yan majalisar Amurka da ke son a soke aiki da Shari'ar Musulunci a wasu jihohin Arewa.

'Yan majalisar sun fadi haka ne a wani rahoto da suka mika ga shugaba Donald Trump, amma Sheikh Gumi ya ce nan gani nan bari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng