Zargin Ta'addanci: Kwankwaso Ya Samu Kariya, an Tura Wasika zuwa Majalisar Amurka

Zargin Ta'addanci: Kwankwaso Ya Samu Kariya, an Tura Wasika zuwa Majalisar Amurka

  • Jam’iyyar NNPP ta rubuta wa Majalisar Dokokin Amurka wasika game da zargin Sanata Rabiu Kwankwaso kan ta'addanci
  • NNPP ta yi hakan ne domin kare ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso bayan zargin da Amurka ke yi masa
  • Shugaban NNPP na ƙasa, Ahmed Ajuji, ya ce an ware Kwankwaso shi kaɗai aka ambata da haka, yayin da sauran da ake zargi kungiyoyi ne kawai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Ahmed Ajuji, ya ce jam’iyyar ta rubuta wa Majalisar Dokokin Amurka wasika ta musamman.

Ajuji ya ce sun yi hakan ne domin kare ɗan takararsu na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso.

NNNP ta tura wasika majalisar Amurka game da zargin Kwankwaso
Shugaba Donald Trump na Amurka da Rabi'u Musa Kwankwaso. Hoto: Donald J Trump, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Ajuji ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai wanda jaridar Punch ta bibiya a ranar Alhamis 5 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Abba da ya yi murabus ya zama Shugaban APC bayan awanni a Kano

Martanin NNPP kan zargin Amurka kan Kwankwaso

Ajuji ya ce jam’iyyar ta gaggauta mayar da martani kan zargin ta'addanci da Amurka ke yi wa Kwankwaso.

Ya ce jam’iyyar ta ɗauki matakin ne domin kalubalantar zargin da ta bayyana a matsayin na siyasa, wanda aka yi domin bata sunan Kwankwaso.

A cewarsa, tsohon gwamnan Kano an ware shi ne shi kaɗai aka ambaci sunansa cikin waɗanda ake zargin suna tallafa wa ta’addanci a Najeriya.

Ajuji ya ce:

“Da fari dai, ka fahimci cewa shi kaɗai ne mutum da aka ambata da haka. Sauran duk kungiyoyi ne kawai aka ambata.”

Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta yi mamakin dalilin da ya sa aka ware Kwankwaso aka saka shi cikin jerin waɗanda ake zargi da tallafa wa ta’addanci.

A cewar shugaban NNPP, batun na cike da ce-ce-ku-ce sosai, kuma akwai alamun cewa zargin na iya kasancewa yana da alaƙa da siyasa.

Ya ce:

“Wannan tambaya ce da ke cike da ce-ce-ku-ce. Zargi ne mai ɗauke da bangaren addini, amma a ƙarshe muna ganin farautar siyasa ce.”

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta tanka bayan 'yan adawa sun yi matsaya kan dokar zabe

NNPP ya kare Kwankwaso kan zargin Amurka
Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso: Musabbabin aika wasika ga majalisar Amurka

Ajuji ya bayyana cewa jam’iyyar ta aika da wasiƙa zuwa ga ‘yan majalisar dokokin Amurka domin bayyana matsayinta kan lamarin tare da wanke Kwankwaso daga zargin.

Ya ce suna da yakinin cewa bayanan da suka gabatar za su taimaka wajen gyara abin da suka kira rashin fahimta da aka samu a lamarin, kamar yadda Sahara Reporters ta ce.

A cewarsa:

“Mun yi imanin cewa idan suka ga bayanan da muka gabatar, za su gane cewa sun yi kuskure a inda suka tsaya.”

Ajuji ya jaddada cewa Kwankwaso ba shi da wata alaƙa da ta’addanci, yana mai cewa a lokacin da ya shugabanci Kano ya nuna yadda yake ƙarfafa zaman lafiya tsakanin addinai.

Amurka: Majalisar Shari'a ta kare Kwankwaso

An ji cewa Majalisar Kolin Shari'a ta Najeriya ta ba Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kariya kan zargin da wani dan majalisar Amurka ya masa.

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya isa": SCSN ta yi raddi da Amurka ta tsoma baki kan shari'ar Musulunci

Ta ce babu gaskiya a zargin da wasu 'yan majalisar Amurka ke yi wa Kwankwaso, tana cewa akwai alamar an dagora da bayanai marasa inganci.

Wani dan majalisar Amurka ya nemi a hana Rabiu Kwankwaso biza da nufin hana shi shiga kasar kan zargin tauye hakkin addini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.