'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojojin Najeriya, Sun Yi wa Limamin Masallaci Yankan Rago

'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojojin Najeriya, Sun Yi wa Limamin Masallaci Yankan Rago

  • 'Yan ta'adda da ake zargin Boko Haram ne sun kai hari sansanin sojoji da na 'yan gudun hijira a Ngoshe da ke Gwoza, jihar Borno
  • Maharan sun yanka babban Limamin garin Ngoshe tare da kona gidaje da motocin yaki bayan dakarun soji sun gaza dakile harin
  • Sanata Ali Ndume ya bukaci rundunar sojoji ta kaddamar da gagarumin samame a dajin Sambisa domin fatattakar yan ta'addan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno - Wasu da ake zargi 'yan ta'addan Boko Haram ne sun kaddamar da munanan hare-hare kan sansanin sojoji da na 'yan gudun hijira dake garin Ngoshe a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun mamaye garin ne bayan da Musulmi suka kammala buda baki a daren Laraba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shammaci 'yan sanda ana azumi, sun yi barna mai girma

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya, sun sace mata da yara a Borno
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Borno: 'Yan ta'adda sun kashe sojoji

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa maharan sun mamaye sansanin sojoji na "82 Division TF Battalion" tare da fatattakar dakarun dake wurin, in ji rahoton Daily Trust.

A yayin wannan hari, an samu labarin cewa 'yan ta'addan sun kashe sojoji da fararen hula da ba a san adadinsu ba.

Zuwa yanzu, an gano gawarwakin sojoji tara daga cikin wadanda aka kashe. Haka kuma, maharan sun kona tankunan yaki da motocin soji tare da sace makamai masu tarin yawa.

Ba su tsaya a nan ba, domin 'yan ta'addan sun shiga cikin garin Ngoshe inda suka kashe babban Limamin garin ta hanyar yanka shi.

'Yan ta'adda sun sace mata, yara

Bayan kisan gillar, maharan sun yi awon gaba da mata da yara sama da 100, kamar yadda rahoton jaridar The Cable ya nuna.

Wannan barna ta hada da kona gidaje da wuraren kasuwanci na jama'a, wanda ya tilasta wa mazauna garin tserewa zuwa garin Pulka dake makwabtaka da su.

Kara karanta wannan

Rana ta 5: Iran ta zafafa hare hare kan Amurka, ta harba makamai masu linzami 40

Majiyoyi sun bayyana fargaba musamman ganin yadda 'yan gudun hijira suka fara dawowa gida daga kasar Kamaru.

Wasu na zargin cewa akwai masu ba da bayanan sirri daga cikin gari wadanda suka taimaka 'yan bindigar suka kaddamar da wadannan hare-hare cikin sauki.

'Yan ta'adda sun kashe sojoji da fararen hula a Borno
Taswirar jihar Borno, inda 'yan ta'adda suka kashe sojoji da fararen hula. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sanata Ndume ya yi martani kan harin

Sanata Ali Ndume, dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu, ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari.

Ndume ya bayyana cewa 'yan ta'addar ba sa jin dadin shirin gwamnati na sake tsugunar da mutane a yankin, shi ya sa suka kaddamar da harin domin tsoratar da jama'a.

Sanatan ya yi kira ga rundunar soji da su gudanar da gagarumin samame a cikin dajin Sambisa da kuma tsaunukan Mandara domin kakkabe ragowar 'yan ta'addan.

Boko Haram ta kashe kwamandan sojoji

A wani labari, mun ruwaito cewa,

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com