Majalisar Dokoki Ta Fara Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo

Majalisar Dokoki Ta Fara Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo

  • An gabatar da kudirin neman tsige Mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Gwarzo a gaban Majalisar dokoki yau Alhamis
  • Shugaban masu rinjaye a Majalisa, Hon. Lawan Hussaini Dala ne ya gabatar da takardar tuhume-tuhumen da ake yi wa Aminu Gwarzo
  • Mai magana da yawun Majalisar, Kamaludden Sani Shawai ya tabbatar wa Legit Hausa an gabatar da takardar tuhume-tuhume, amma ba tsige shi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo a zaman ta na yau Alhamis, 5 ga Maris, 2026.

Majalisar dokokin ta fara wannan yunkuri ne bisa zargin Aminu Gwarzo da hannu a badakalar kudin al'umma lokacin da yake rike da kwamishinan kananan hukumomin Kano.

Mataimakin gwamnan Kano.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo Hoto: Comrd Aminu Abdulsalam Gwarzo
Source: Twitter

Majalisa ta fara shirin tsige Aminu Gwarzo

Kara karanta wannan

Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa ‘yan majalisar sun ce zarge-zargen na da nasaba da yadda aka gudanar da wasu harkokin kudi, wanda suke ganin ya saba wa ka’idojin shugabanci.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano, Hon. Lawan Hussaini Dala, ne ya gabatar da takardar kudirin tsige mataimakin gwamnan a zaman yau Alhamis.

Ya bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, musamman sashe na 188 da ya tanadi yadda ake tsige manyan jami’an gwamnati.

Zarge-zargen da ake yi wa Mataimakin gwamnan Kano

A cewarsa, zarge-zargen sun shafi lokacin da Aminu Gwarzo ya rike mukamin Kwamishinan Kananan Hukumomi na Kano tsakanin 2023 zuwa 2024 da harkokin ofishinsa na mataimakin gwamna.

Hon. Lawan Dala ya bayyana cewa a lokacin da yake jagorantar ma’aikatar kananan hukumomi 44 na Kano, an zarge shi da karbar Naira miliyan 1.5 duk wata daga kowace karamar hukuma tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Janairun 2024.

Wannan, a cewarsa, ya kai kimanin Naira miliyan 66 a kowane wata, wanda jimillarsa gaba daya ta kai kusan Naira miliyan 462, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Abba da ya yi murabus ya zama Shugaban APC bayan awanni a Kano

Bayan wannan kuma, shugaban masu rinjaye ya ce daga watan Fabrairu zuwa Yulin 2024, ana zargin kowace karamar hukuma ta sake ware wa Aminu Gwarzo Naira miliyan 3.255 a wata da sunan gudanar da wasu ayyuka na musamman.

A cewarsa, kudin da aka tarawa mataimakin gwamnan a cikin watanni shida sun kai kusan Naira miliyan 726.

Majalisa ta fara cika sharuddan tsige Aminu Gwarzo

Ya ce irin wadannan mu’amaloli sun saba wa dokokin mu'amala da kudaden gwamnati, kuma suna daga cikin manyan laifuffuka a karkashin kundin tsarin mulki, domin sun karya amana da ka’idojin da ake bukata daga jami’in gwamnati.

Lawan Dala ya kuma bayyana cewa ‘yan majalisa 38 ne suka sanya hannu kan kudirin tsige mataimakin gwamnan, abin da ya cika sharadin da doka ta tanada domin fara wannan tsari.

Shugaban majalisar, Rt. Hon Isma'ila Falgore ya amshi takardar kudirin, kuma ana sa ran za a mika ta ga Mataimakin gwamnan domin ya kare kansa bisa tsarin da doka ta gindaya.

Majalisar Kano.
Zauren Majalisar dokokin jihar Kano yayin zama kamar yadda doka ta tanada Hoto: Kamal Ibrahim Hotoro
Source: Facebook

An kai ga tsige Mataimakin gwamnan Kano?

Legit Hausa ta tuntubi mai magana da yawun Majalisar dokokin Kano, Kamaludden Sani Shawai, wanda ya tabbatar mana da cewa an gabatar da tuhume-tuhumen da ake wa Aminu Gwarzo.

Kara karanta wannan

Yadda kisan Khamenei zai shafi 'yan Shi'a a Najeriya, rashinsa ya 'hada' kan Musulmi

Shawai ya shaidawa wakilinmu ta wayar tarho cewa labarin da wasu jaridu ke yadawa cewa an tsige mataimakin gwamnan ba gaskiya ba ne, domin dole sai an bi matakai.

"Abin da ya faru shi ne gabatar da takarda ta tuhume-tuhume, wadanda ake ui wa mataimakin gwamnan Kano, amma ba wai an tsige shi ba, akwai matakai da za a bi bisa kundin tsarin mulki,"

- in ji Kamaludden Sani Shawai.

Kwamishina ya yi murabus a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Hon. Umar Haruna Doguwa ya yi murabus daga kujerar kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din kwamishinan, tare da yaba masa bisa gudummuwar da ya ba gwamnatinsa da al'ummar Kano.

Abba ya masa fatan alheri a ayyukansa na gaba, sannan ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da dora wa kan nasarorin da aka samu a bangaren albarkatun ruwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262