Yan Sandan Jihohi: Sabon Shugaban Rundunar Ya Dauko babban Aiki kan Tsaro

Yan Sandan Jihohi: Sabon Shugaban Rundunar Ya Dauko babban Aiki kan Tsaro

  • Sufeto Janar na ‘yan sanda, Tunji Disu, ya kafa kwamitin mutum bakwai domin tsara yadda za a aiwatar da tsarin ‘yan sandan jihohi a Najeriya
  • Kwamitin karkashin jagorancin Farfesa Olu Ogunsakin zai duba batutuwan daukar ma’aikata, horaswa, rabon kayan aiki da kuma hanyoyin sa ido mai inganci
  • Shugaba Bola Tinubu ya bukaci majalisar tarayya ta gyara kundin tsarin mulki na 1999 domin samar da cikakken tsarin doka ga ‘yan sandan jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sabon sufeto-janar na yan sanda, Tunji Disu ya shirya ƙaddamar da yan sandan jihohi a Najeriya domin kara tsaro a kasa.

Disu ya kaddamar da kwamitin mutum bakwai domin kula da aiwatar da tsarin ‘yan sandan jihohi a Najeriya.

An kafa kwamitin yan sandan jihohi
Sabon shugaban yan sanda, Tunji Disu da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Bukatar Disu ga kwamitin da ya kafa a Abuja

Kara karanta wannan

Yadda kisan Khamenei zai shafi 'yan Shi'a a Najeriya, rashinsa ya 'hada' kan Musulmi

An kaddamar da kwamitin ne ranar Laraba 4 ga watan Maris, 2026 inda Farfesa Olu Ogunsakin, kwararre a fannin nazarin aikin ‘yan sanda, zai jagoranci aikin kwamitin, cewar Vanguard.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwa, Disu ya bukaci kwamitin ya samar da tsari na aiki mai inganci domin kafawa da daidaita ‘yan sandan jihohi.

Ya ce dole kwamitin ya duba batutuwan horaswa, daukar ma’aikata, rabon kayan aiki da kuma samar da hanyoyin sa ido masu karfi.

Disu ya bayyana cewa rabon iko ga jihohi zai taimaka wa gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi magance matsalolin tsaro cikin sauri.

Ya ce:

“Ina mai matukar farin ciki na kaddamar da wannan kwamiti kan ‘yan sandan jihohi domin karfafa tsarin tsaron Najeriya.”

Ya kara da cewa aikin kwamitin yana da matukar muhimmanci, domin zai taimaka wajen tsara yadda tsarin zai karfafa hadin kan tsaron kasa.

An kafa kwamitin kafa yan sandan jihohi
Sufeta-janar na yan sanda a Najeriya, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Bode Ojajuni a matsayin sakatare, Okebechi Agora, Suleyman Gulma, Ikechukwu Okafor, Tolulope Ipinmisho da Emmanuel Ojukwu.

Musabbabin shirin kafa yan sandan jihohi

Shugaba Bola Tinubu ya sha alkawarin kafa ‘yan sandan jihohi domin magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Kara karanta wannan

Fasto ya kare kansa game da zuwa Makka da Madina, ya magantu kan zama Musulmi

Kwanan nan, ya bukaci majalisar tarayya ta gyara kundin tsarin mulki na 1999 domin samar da doka da za ta ba da damar kafa ‘yan sandan jihohi.

Majalisar tarayya ta fara aikin gyaran kundin tsarin mulki na 1999 domin bai wa jihohi damar kafa nasu rundunar ‘yan sanda, cewar Punch.

Ana ta kokarin kafa yan sandan jihohi duk da korafe-korafe da ake yi kan lamarin saboda ana ganin za a iya amfani da su ta hanyoyin da ba su dace ba.

Jingir ya kalubalanci shirin kafa yan sanda jihohi

A baya, mun ba ku labarin cewa Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nuna adawa da shirin kafa ‘yan sandan jihohi.

Sheikh Jingir ya yi gargadin akwai yiwuwar amfani da su don murkushe abokan adawa a Plateau wanda ba zai zama da dadi ba.

Malamin ya roki Bola Ahmed Tinubu da ya yi taka-tsantsan kafin amincewa da tsarin ‘yan sandan jihohi a fadin kasar duba da yadda ake fatali da lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.