Malamin Addini a Najeriya Ya Yi Hasashen Wanda Zai Samu Nasara a Yakin Iran da Amurka

Malamin Addini a Najeriya Ya Yi Hasashen Wanda Zai Samu Nasara a Yakin Iran da Amurka

  • An gargadi Amurka da Isra'ila cewa watakila ba za su yi nasara a yakin da suke yi da Iran ba, bayan kisan Jagoran Kolin Iran, Ali Khamenei
  • Isra’ila da Amurka ne suka fara kai wa Iran hari, lamarin da limamin coci a Nijeriya, Elijah Ayodele, ya yi hasashen zai iya janyo tangardar tattalin arzikin
  • Ayodele ya fadi haka ne bayan tsohon hasashen marigayi babban limamim coci, TB Joshua ta sake bayyana a kafafen sada zumunta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Primate Elijah Ayodele, jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church da ke Oke Afa, Legas, ya yi hasashen wanda zai samu nasara a yakin Iran da Amurka da Isra'ila.

Fitaccen limamin coci a Najeriya ya ce Amurka da Isra'ila ba za su yi nasara a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ba, wadanda suka fara farmakar Iran.

Kara karanta wannan

Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Babban limamin coci, Fasto Ayodele.
Fitaccen malamin coci a Najeriya, Primate Elijah Ayodele Hoto: Primate Ayodele
Source: Twitter

Ayodele ya bayyana haka ne a wani bidiyo da IESC Worldwide ta wallafa a shafin Facebook, inda aka ga malamin na jawabi a cocinsa da ke jihar Legas.

Yadda aka kashe Ayatollah Ali Khamenei

Wannan hasashen na zuwa ne bayan hare-haren soji da Amurka da Isra’ila suka kai a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, inda suka kashe Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Mutuwar Khamenei ta kara haddasa matsananciyar rigima a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da gwamnatin Iran ta yi alkawarin daukar fansa.

Shugaban kasa Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa rundunar sojojin Iran za ta ruguza sansanonin makiya a yankin, tare da kiran rasuwar Khamenei a matsayin “ayyana yaki da Musulmai."

Fasto Ayodele ya hango abin da zai faru

Primate Ayodele, a cikin jawabi da ya yi a coci, ya ce Amurka ba za ta ci nasara a wannan yaki ba kuma Shugaba Donald Trump ba zai cimma burinsa ba kamar yadda ya yi a kan Venezuela.

Kara karanta wannan

Yadda dan Khamenei da zai iya gadonsa, Mojtaba ya tsallake harin Amurka da Isra'ila

Ya ce Trump da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu za su yi nadama kan abin da suka aikata na kai hari kan Iran.

Ayodele ya yi hasashen cewa Iran za ta sake fuskantar Amurka kai-tsaye kuma yakin ba zai kare cikin kankanin lokaci ba, sannan ya ce ba za a cimma maslahar siyasa ba sai bayan dogon lokaci.

Ya kara da cewa tun da farko ya yi gargaɗi cewa rikicin zai iya janyo matsalar tattalin arzikin duniya, saboda kai hari kan Iran na da matukar illa.

Netanyahu da Trump.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu lokacin da ya ziyarci Shugaba Donald Trump a Amurka Hoto: Anadolu
Source: UGC

Hasashen Fasto T. B Joshua ya bayyana

Hasashen Ayodele ya zo ne bayan sake bayyanar faifan bidiyo na marigayi T.B Joshua, inda ya yi hasashen illolin yaki tsakanin Isra’ila da Iran. Wani mai suna Olaudah Equiano ya wallafa bidiyon a X.

A cikin wannan bidiyo da aka dauka a 2012, T.B Joshua, babban malamin coci a Najeriya ya roki mabiyansa da su yi addu’a don a hana barkewar yaki tsakanin wadannan kasashe.

Ya ce rikicin Amurka, Isra'ila da Iran zai iya janyo Yakin Duniya na Uku mai muni, fiye da yadda ake tsammani. Ya kuma yi kira ga shugabannin duniya da su dauki matakin hana wannan yaki.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta fadi wani babba da ta ke shirin hallaka wa a kasar Iran

Amurka ta gargadi yan kasarta a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa ana fargabar barkewar zanga-zanga a birnin Abuja game da rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya bayan Amurka da Iran sun kashe jagoran Iran.

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya soke duk wata ganawa da masu neman biza da aka tsara bisa hasashen yiwuwar zanga-zanga a birnin.

Har ila yau, ofishin ya kuma gargadi ‘yan kasar Amurka da su zauna a cikin gidajensu, su guji wuraren da ake tattaunawa ko za a yi gangami a Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262