Kotu Ta Dauki Sabuwar Matsaya a Shari'ar Abubakar Malami da Dansa

Kotu Ta Dauki Sabuwar Matsaya a Shari'ar Abubakar Malami da Dansa

  • Ana ci gaba da fafatawa tsakanin lauyoyin gwamnati da na tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, a shari'ar zargin daukar nauyin ta'addanci
  • A yayin zaman kotu na ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026, masu shigar da kara sun gabatar da sabuwar bukata a gaban kuliya
  • Lauyoyin wadanda ake kara ba su kalubalanci bukatar ba, amma sun yi kira da a yi watsi da karar idan har ba su yi abin da suka ce za su yi ba

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage shari’ar zargin daukar nauyin ta’addanci da ake yi wa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami.

Kotun ta dage shari'ar da ake yi da tsohon Ministan tarayya kuma tsohon babban lauyan gwamnati (AGF) da dansa zuwa ranar 10 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Rana ta 5: Iran ta zafafa hare hare kan Amurka, ta harba makamai masu linzami 40

Kotu ta dage karar Abubakar Malami kan zargin daukar nauyin ta'addanci
Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami, SAN
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa kotun ta dage shari'ar ne a ranar Laraba, 4 ga watan Maris 2028.

DSS ta gurfanar da Abubakar Malami gaban kotu

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce ta gurfanar da Malami da ɗansa, Abdulaziz, a ranar 3 ga watan Fabrairu, bisa tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin ɗaukar nauyin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar DSS ta zargi Malami da ƙin gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci, waɗanda aka ce an tura takardar shari’arsu zuwa ofishin babban lauyan gwamnati domin a hukunta su.

A ranar 27 ga watan Fabrairu, kotu ta bayar da belin tsohon AGF ɗin da ɗansa a kan kuɗi Naira miliyan 200 kowannensu, tare da mutane biyu da za su tsaya musu a kan kuɗi ɗaya.

Masu shigar da kara na bukatar karin lokaci

Yayin da aka ci gaba da shari’ar a ranar Laraba, Rotimi Oyedepo, ya shaida wa kotun cewa an mayar da takardar shari’ar zuwa sashen DPP na ma'aikatar shari'a, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Alkali ta amince da bukatar Abubakar Malami da dansa, an kafa sharadi a kotu

Oyedepo ya bayyana cewa masu shigar da karar suna buƙatar ƙarin lokaci domin su fahimci hujjoji da bayanan da ke cikin shari’ar sosai.

Adedayo Adedeji, lauyan da ke kare waɗanda ake ƙara, bai nuna rashin amincewa da wannan buƙatar ba.

Kotu ta dage sauraron shari'ar Abubakar Malami
Abubakar Malami zaune a cikin harabar kotu Hoto: @OfficialEFCCNg
Source: Twitter

An bukaci kotu ta yi watsi da karar

Amma ya buƙaci kotun da ta yi watsi da shari’ar idan har masu shigar da ƙara suka kasa fara shari’ar zuwa ranar da aka dage ta, inda ya kafa hujja da rashin nuna ƙwazo wajen gudanar da shari’ar.

Mai shari'a Joyce Abdulmalik, wadda take jagorantar shari’ar, ta ɗage karar zuwa ranar 10 ga watan Maris domin fara sauraron shari’ar gadan-gadan.

Kotu ta tura Malami gidan yari

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta ba da umarnin tsare tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami a gidan yari.

Alkalin kotun mai shari'a Joyce Abdulmalik ta aika da Malami tare da matarsa, Hajiya Bashir Asabe, da dansu, Abubakar Abdulaziz Malami, zuwa gidajen yari har sai an yanke matsaya kan bukatar belinsu.

Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa an soke belin da aka ba su a baya tun da an canza alkali da kuma kotun da ke sauraren karar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng