An Dakatar da Sheikh Salihu Zaria daga Gabatar da Tafsirin Kur'ani a Damaturu

An Dakatar da Sheikh Salihu Zaria daga Gabatar da Tafsirin Kur'ani a Damaturu

  • Kungiyar Izala ta dakatar da Sheikh Salihu Zaria daga tafsiri a Damaturu saboda yin amfani da kalaman jafa'i ga shugabanni da jami'an tsaro
  • Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayar da umarnin dakatar da malamin domin kiyaye manufofin kungiyar da kuma tabbatar da tsaron kasa
  • Alkali Zaria ya nemi gafarar al'umma tare da bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa mai biyayya ga shugabancin kungiyar Izala ta reshen Jos

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jos - Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) mai hedikwata a Jos, ta dakatar da Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria daga ci gaba da tafsiri a birnin Damaturu.

Sanarwar, wadda ta fito daga reshen ƙungiyar na jihar Yobe, ta nuna cewa matakin ya biyo bayan umarnin Shugaban majalisar malamai na ƙasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir.

Kara karanta wannan

Halin da maniyyata ke ciki yayin da rikicin Iran da Isra'ila ke kara ta'azzara

Izala ta dakatar da Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria daga tafsirin Alkur'ani a Damaturu.
Sheikh Sani Yahaya Jingir tare da Sheikh Alkali Salihu Zaria a ganawar da suka yi kan dakatar da malamin daga tafsiri. Hoto: Jibwis NHQ Jos - Damaturu
Source: Facebook

An dakatar da Alkali Zaria daga Tafsir

Sheikh Sani Yahya Jingir ya ba da umarnin dakatar da Alkali Zaria ne saboda dalilai da suka shafi tsaro da kuma kiyaye manufofin ƙungiyar, cewar sanarwar da aka wallafa a shafin kungiyar na Facebook.

Sheikh Alkali Zaria, wanda aka turo daga Jos domin gudanar da tafsirin bana a Damaturu, ya shafe kwanaki 11 yana karatu kafin aka dakatar da shi a ranar 12 ga watan Ramadan.

Sanarwar ta nuna cewa kalaman da malamin ya yi a wurare daban-daban, ciki har da hedikwatar ƴan sanda ta jihar Yobe da kuma masallacin Mokas inda yake sanye da kayan agaji, sun haifar da ce-ce-ku-ce.

Izala ta bayyana salon wa'azin nasa, wanda ya haɗa da kiran sunayen mutane, tsinuwa, da kalaman jafa'i ga jami'an tsaro da shugabanni, a matsayin wanda ya saɓa wa koyarwar ƙungiyar.

Dalilan dakatar da Alkali Zaria

Kara karanta wannan

Iran/Isra'ila: Izalah ta magantu kan fara Al Kunut a masallatai, ta tabo matsalolin Najeriya

Sanarwar ta jero dalilan da suka sanya aka dakatar da Alkali Zaria kamar haka:

  1. Huduba da nasihar da malamin ya yi a jihar Yobe a hedikwatar 'yan sanda ranar Juma'ar da ta gabata.
  2. Nasihar da malamin ya yi bayan an idar da Sallar Asuba a masallacin Alimarami, a ranar Asabar.
  3. Tafsirin da ya yi a ranar Juma'a da daddare sanye da kayan agaji, a masallacin Mokas inda yake gabatar da Tafsiri.

Sanarwar ta ce:

"Lallai, hakika wadannan abubuwa sun shafi al'umma da yawa, ciki akwai jami'an tsaro, gwamnoni, har da shugaban kasa.
"Irin wannan salon da mallam ya yi amfani da shi na kiran sunayen mutane, da tsinuwa, da jafa'i, ya sabawa karantarwar kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a wa Iqamatissunnah."

Abin da Sheikh Salihu Zaria ya ce

Sheikh Salihu Zaria ya ce zai yi biyayya ga duk matakin da Izala ta dauka.
Sheikh Sani Yahaya Jingir tare da Sheikh Alkali Salihu Zaria da tawagar Izala ta Damaturu a Jos. Hoto: Jibwis NHQ Jos - Damaturu
Source: Facebook

Bayan dakatar da shi daga tafsirin Alkur'ani, fitaccen malamin ya fito ya yi magana a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa:

"Inaso kowa ya sani cewa, ni dan kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah wa Ikamatis Sunnah ne NHQ Jos karkashin jagoranchin Fhadilatush Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ne.

Kara karanta wannan

Iran: Amurka ta yi magana kan Najeriya bayan zanga zangar 'yan Shi'a

"Sannan kuma ba ni ne na kai kai na Damaturu ba, kungiya ce ta turani a matsayin mai tafsir na wannan shekarar 1447/2026.
"Na karbi wannan umurni na shugabanmu babanmu malaminmu fadilatush Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir da sunan Allah.
"Yan uwana da abokai na, masoya da kowa da kowa, ina mai baiwa kowa hakuri akan wannan al'amari, wa'adin da Allah ya rubuto mun da zan yi a Damaturu iya lokachin da Allah ya kaddara mun kenan."

Karanta sanarwar malamin a nan kasa:

Muguwar addu'o'in Abubakar Zaria ga shugabanni

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya yi addu’a mai zafi ga azzaluman shugabanni a gaban Peter Obi, a ziyarar da ya kai Kaduna.

A lokacin da Peter Obi ya ziyarci cibiyoyin ilimi a Kaduna, malamin ya yi addu’ar Allah ya karɓi ran shugabannin da ba alheri ba ne kafin lokacin zaɓe.

Sheikh ya bayyana cewa cancanta, ba addini ba, ya kamata a duba wajen zaɓen shugabanni a zaben Najeriya na 2027 da ke tafe domin samun ci gaba da daidaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com