Matar El Rufa'i Ta Lissafa Na'urorin da Jami'an ICPC Suka Kwashe daga Gidansu
- Hadiza Isma El-Rufai, matar tsohon gwamnan Kaduna ta ce ICPC ta kwashe mata wasu muhimman na'urorin yayin bincike a gidansu
- Tana zargin hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati mai zaman kanta ta ICPC ba ta saka na’urorin cikin jerin kayayyakin ta kwato ba
- Hajiya Hadiza Isma ta bayyana haka ne a yayin da ICPC ta yi ikirarin cewa ta samu wasu na'urorin kutsen waya a gidan Nasir El-Rufa'i
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja– Uwargidan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai, ta nuna damuwa kan yadda jami’an CPC suka gudanar da bincike a gidansu.
A cewarta, a lokacin samamen da aka kai gidansu, jami’an hukumar sun dauke mata na’urorin tsaro na banki.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Hadiza Isma ta yi zargin cewa amma ba su bayyana hakan cikin jerin kayayyakin da suka fitar a hukumance ba.
ICPC ta samo kaya a ofishin ICPC
Imran Wakili ya wallafa a shafin X cewa tun da farko, ICPC ta wallafa bayanin kayayyakin da ta ce ta kwato yayin aikin binciken. Sai dai a cikin jerin, ba a ambaci na’urorin banki ba.
Rahotanni sun nuna cewa wannan gibi ne ya sa matar El-Rufai ta dauki matakin yin magana a bainar jama’a.
Hadiza Isma El-Rufai ta bayyana cewa akwai yiwuwar a samu rudani dangane da irin wadannan kananan na’urori, musamman duba da maganganun da ke yi

Source: Facebook
Tun bayan ziyarar da jami'an ICPC suka kai gidan El-Rufa'i suka ce sun ga wasu kayayyaki da aka bayyana a matsayin na’urorin sa ido.
A wani sako da ta fitar, Hadiza Isma El-Rufai ta ce:
"Kun manta ku saka cewa sun ɗauki na'urorin bayanan banki na, Na rantse da Allah ba kayan kutsen sauraron waya ba ne."
Zargin matar El-Rufai kan ICPC
Hadiza Isma El-Rufai na zargin cewa an manta da ambaton cewa an dauke mata na’urorin banki, tare da jaddada cewa ba kayan satar bayanai ko sauraren waya ba ne.
Ta kuma hada hoton wasu kananan na’urori guda uku, wadanda aka fi sani da "electronic banking tokens".
Ana amfani da wadannan na’urori domin tabbatar da ma’amalolin kudi ta yanar gizo, tare da kara wani matakin tsaro ga asusun banki.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumar ICPC ba ta fitar da karin bayani kai tsaye kan zargin da matar El-Rufai ta yi ba.
El-Rufa'i ya ki cewa jami'an ICPC komai
A baya, kun samu labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce binciken da hukumar ICPC ke yi masa yana da alaka da siyasa.
A lokacin da jami'an hukumar suka matsa masa da tambayoyi a kan zarge-zagen da ake yi masa, El-Rufa'i ya ki ba hadin kai, inda ya ce ba zai ce masu komai ba.
Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta ce tana binciken tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i a kan zargin karkatar da kudi da karya dokokin kwangila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

