Dangote Na Shirin Bunkasa Arzikinsa, Ya Fadi Wasu Fannoni 3 da Zai Shiga

Dangote Na Shirin Bunkasa Arzikinsa, Ya Fadi Wasu Fannoni 3 da Zai Shiga

  • Hamshakin attajirin dan kasuwa a Afrika, Aliko Dangote, na shirin fadada harkokin kasuwancinsa zuwa wasu fannoni
  • Dangote na shirin shiga fannin samar da wutar lantarki, karafa don bunkasa samar da masana'antu a nahiyar Afrika
  • Babban dan kasuwar ya kuma bayyana cewa ana shirin kara fadada matatarsa mai tace gangar mai 650,000 a kowace rana

​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana shirinsa na faɗaɗa kasuwancinsa.

Dangote na da shirin fadada kasuwancinsa zuwa fannin samar da karafa, samar da wutar lantarki, da kuma haɓaka tashoshin jiragen ruwa, a matsayin wani ɓangare na babban burinsa na hanzarta bunƙasa masana'antu a faɗin Afirka.

Dangote zai shiga fannin samar da lantarki
Hamshakin dan kasuwa kuma attajiri, Aliko Dangote Hoto: Aliko Dangote
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da New York Times.

Burin Dangote kan nahiyar Afrika

Kara karanta wannan

Bayan komawa APC, Gwamna ya sace gwiwoyin 'yan Arewa kan zaben shugaban kasa a 2027

Dangote, wanda rukunin kamfanoninsa ya mamaye fannonin siminti, sukari, gishiri, taki, da matatun mai, ya bayyana cewa burinsa na dogon lokaci shi ne ƙarfafa tushen masana'antun Afirka fiye da tace mai kawai.

Babban aikinsa na yanzu, wato matatar mai tuni ta fara aiki inda take samar da kusan ganga 650,000 na tataccen mai a kullum.

Ya bayyana cewa ana sa ran samun ƙaruwar wannan adadin zuwa ninki biyu a cikin shekaru uku masu zuwa yayin da shirye-shiryen faɗaɗa ta ke ci gaba.

Dangote ya nuna cewa tace mai wani mataki ne kawai na babban burin da yake da shi wajen bunkasa nahiyar Afrika.

Wadanne fannoni Dangote zai shiga?

Ya bayyana cewa fannonin da zai mayar da hankali a kai nan gaba sun haɗa da masana'antar karfe, faɗaɗa hanyoyin samun wutar lantarki, da gina ƙarin tashoshin jiragen ruwa domin tallafa wa manyan masana'antu da kasuwanci.

Dangote ya buga misali da rukunin kamfanonin Tata Group na ƙasar Indiya a matsayin abin koyi ga faɗaɗa kasuwanci, inda ya bayyana yadda manyan masana'antu za su iya sauya fasalin tattalin arziƙin ƙasashe masu tasowa.

Kara karanta wannan

Yadda yakin Iran, Amurka da Isra'ila zai jawo tarnaki a Najeriya

Baya ga faɗaɗa kasuwanci, Dangote ya ce samar da ayyukan yi shi ne babban jigon tsarinsa, jaridar The Guardian ta kawo labarin.

Dangote zai fadada harkokin kasuwancinsa
Wani bangare na matatar man Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Najeriya na bukatar karin masana'antu

Ganin yadda ake hasashen cewa Najeriya za ta buƙaci sababbin ayyukan yi tsakanin miliyan 40 zuwa 50 nan da shekarar 2030, ya bayyana cewa manyan ayyukan masana'antu ne kawai za su iya ɗaukar dimbin matasan ƙasar da ke ƙaruwa.

A halin yanzu, matatar man tana ɗauke da ma’aikata kusan 30,000, inda kashi 80 cikin 100 daga cikinsu ’yan Najeriya ne.

Ana sa ran cewa faɗaɗa kasuwancin zuwa sababbin fannoni zai ƙara yawan ma'aikatan rukunin kamfanonin zuwa kusan 65,000.

Matatar Dangote ta kara farashin man fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote ta kara farashin da take sayar da fetur ga 'yan kasuwa.

Matatar Dangote ta kara kara farashin sayarwa daga N774 zuwa N875 kan kowace lita ga 'yan kasuwar da suke saya a wajenta.

Wani babban jami'i a matatar ya bayyana cewa karin ya biyo bayan rashin tabbas da aka samu a farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng