Babbar Magana: Yakin Kasar Iran da Amurka, Isra'ila Ya Fara Taba 'Yan Najeriya
- Yakin Iran da Amurka/Isra'ila ya fara shafar yan Najeriya yayin da aka ruwaito cewa farashin litar fetur ya kama hanyar N1,000 a Abuja da Legas
- Wannan dai na zuwa ne biyo bayan karin kudin sari na kowace lita da matatar Dangote ta yi a ranar Litinin, 2 ga watan Maris, 2026
- Ana fargabar cewa farashin zai iya ci gaba da hauhawa duba da cewa babu alamun karshen yakin Iran da Amurka, wanda aka fara ranar Asabar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rikicin da ke kara tsananta tsakanin Amurka, Isra'ila, da Iran, wanda ya kusan dakatar da harkoki a Gabas Ta Tsakiya, ya fara shafar 'yan Najeriya.
Idan ba ku manta ba, yaki ya barke tsakanin Amurka, wacce ta hada gwiwa da Isra'ila da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar Asabar da ta wuce, 28 ga watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran

Source: Getty Images
Daily Trust ta tattaro cewa wannan yaki da ya barke, wanda aka shiga rana ta hudu a yau Talata, ya fara taba 'yan Najeriya yayin da gidajen mai suka fara sauya farashin man fetur (PMS).
Farashin litar fetur ya tashi a Najeriya
Bayan tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya, matatar mai ta Dangote, a ranar Litinin, ta kara N100 kan kowane lita, inda ta mayar da farashin sari daga N774 zuwa N874.
Sakamakon haka, gidajen mai a fadin kasar nan suka fara sauya nasu farashin litar fetur, lamarin da zai shafi talakawan Najeriya kai tsaye.
A babban birnin tarayya, Abuja, wasu gidajen mai na kamfanin NNPC sun kara farashin lita daya daga N875 zuwa N960.
A Legas kuma bincike ya nuna cewa gidajen NNPC ba sa sayar da mai, amma sauran gidajen mai na yan kasuwa sun kara farashi. Misali, gidan mai na Bovas ya kara daga N835 zuwa N935
Dalilin tashin farashin fetur a Najeriya
Ana fargabar cewa farashin zai iya ci gaba da hauhawa duba da cewa babu alamun karshen yakin Iran da ya barke bayan harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila, wanda ya yi sanadiyar mutuwar jagoran Iran, Ayatollah Khamenei.
Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare akai-akai kan sansanonin sojin Amurka da kawayenta a makwabtan kasashen Gabas Ta Tsakiya kamar su UAE, Qatar, Bahrain, da Saudiyya.

Source: Getty Images
Hakan ya zama sanadin dakatar da zirga-zirgar danyen mai a duniya, wanda ya sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Bayanai sun nuna cewa gangar danyen mai samfurin Brent Crude ya haura $80 a ranar Litinin, kuma a halin yanzu ana sayar da ganga daya kan $84.2.
Duk da cewa wannan yana nufin karuwar kudaden shiga ga gwamnatin Najeriya, ga talaka kuma yana nufin karin tsadar rayuwa da tashin farashin kayayyaki.
Wani dan mai sayar da mai a bakin titi da aka fi sani da dan bunburutu ya tabbatar wa Legit Hausa cewa man fetur ya yi tashin gwauron zabo a gidajen mai.
Kabiru Dogo, wanda ke sana'arsa a garin Dabai, ya ce zuwa ranar Lahadi, 8 ga watan Maris, 2026, litar fetur ta haura N1,000 a gidan mai.
"Fetur ya haura N1000 a nan jihar Katsina, wannan babbar matsalaa ce da za ta shafi talaka kai tsaye, to amma galibin mutane suna goyon bayan Iran, sun shirya kowace wahala idan har musulunci zai samu nasara," in ji shi.
Matatar Dangote ta kara farashin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa matatar man Dangote ta kara farashin fetur da N101, inda kowace lita ta tashi daga N774 zuwa N875 a rumbunan ajiyarta a a Najeriya.
Wannan ƙarin farashi ya zo ne jim kaɗan bayan da matatar ta dakatar da loda man fetur tun tsakar daren 1 ga Maris, 2026, sakamakon tashin farashin ɗanyen mai a duniya.
Wani babban jami’i a matatar ta Dangote ya tabbatar da cewa wannan canji ya biyo bayan rashin tabbas da aka samu a farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

