Yakin Iran da Amurka Zai Shafi Najeriya, Dangote Ya Kara Farashin Man Fetur

Yakin Iran da Amurka Zai Shafi Najeriya, Dangote Ya Kara Farashin Man Fetur

  • Farashin man fetur zai iya yin tashin gwauron zabi bayan matatar man Dangote ta kara kudi a kan yadda take sayarwa ga 'yan kasuwa
  • Matatar ta Dangote ta kara farashin da take sayarwa ga 'yan kasuwa fiye da N100 kan yadda take sayarwa a baya
  • Karin farashin na man fetur dai na zuwa ne yayin da ake gwabza fada a Gabas ta Tsakiya, wanda hakan ya sa farashin danyen mai ya tashi a duniya

​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Matatar man Dangote ta kara farashin man fetur da Naira 101, inda ta kara farashin sayarwa daga N774 zuwa N875 kan kowace lita.

Wannan mataki ya kara fargabar sake samun ƙarin farashin mai a faɗin ƙasar nan.

Dangote ya kara farashin man fetur
Motocin daukar mai a matatar Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Wani babban jami’i a matatar ya tabbatar wa jaridar The Punch hakan a ranar Litinin, 2 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Yadda yakin Iran, Amurka da Isra'ila zai jawo tarnaki a Najeriya

Meyasa Dangote ya kara farashin fetur?

Jami'in ya bayyana cewa wannan canji ya biyo bayan rashin tabbas da aka samu a farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

“Haka ne, an sake duba farashin. Sabon farashin yanzu shi ne N875 kowace lita maimakon N774."
"Sake duba farashin ya zama dole saboda sauye-sauyen da aka samu a farashin ɗanyen mai na duniya."

- Wani jami’in matatar

Sabon farashin fetur ya fara aiki

Binciken da Legit Hausa ta yi a shafin petroleumprice.ng ya tabbatar da cewa an riga an fara amfani da sabon farashin, wanda ke nuna sauyi a ma'aunin farashin mai na cikin gida.

Wannan ƙarin farashi ya zo ne jim kaɗan bayan da matatar ta dakatar da loda man fetur tun tsakar daren 1 ga Maris, 2026, sakamakon tashin farashin ɗanyen mai a duniya, wanda ya haura $80 kan kowace ganga a cikin dare ɗaya.

Bayanan da aka samu daga majiyoyin masana'antar sun nuna cewa an daina dakon man fetur daidai ƙarfe 12:00 na dare, inda aka dakatar da ɗaukar kaya da kuma bayar da takardun biyan kuɗi, alamar cewa an dakatar da sababbin cinikayya na ɗan lokaci.

Kara karanta wannan

Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026

Sai dai, wannan dakatarwa ta shafi man fetur ne kawai, yayin da aka ci gaba da loda man dizal (AGO) ba tare da tsayawa ba.

'Yan kasuwa za su kara farashin mai

Matakin na matatar Dangote ya kuma janyo martani a fannin kasuwancin mai, inda masu gidajen mai na kashin kansu da dama a faɗin ƙasar suka dakatar da sayar da man fetur a lokacin cinikin ranar.

Matatar Dangote ta kara farashin litar man fetur
Motocin daukar fetur a matatar Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook
“Masu gidajen mai da dama sun dakatar da sayar da man fetur saboda tashin farashin ɗanyen mai. Kasuwar tuni tana la'akari da haɗarin da ke tattare da hakan."
"Babu wanda yake son sayarwa ƙasa da kuɗin da zai sake siyo kaya."

- Wani ɗan kasuwar mai

Wannan ci gaba ya zo ne a daidai lokacin da kasuwar man fetur ta duniya ke fuskantar rashin tabbas sakamakon takaddama tsakanin Amurka da Iran, wanda ya haifar da fargabar katsewar hanyoyin samar da mai, musamman a mashigar ruwa ta Strait of Hormuz.

Dangote zai rika fitar da lita miliyan 65

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar man Dangote ta kulla yarjejeniya da wasu manyan kamfanonin mai 12.

Kara karanta wannan

Kotu a Amurka ta yanke wa tsohon jami’in NNPCL hukunci kan cin hancin $2.1m

Matatar ta Dangote ta kammala yarjejeniya da manyan kamfanonin mai 12 domin rarraba litar fetur miliyan 60 zuwa 65 a kowace rana a fadin Najeriya.

Dangote ya ce tsarin zai tabbatar da samun fetur a ko ina cikin Najeriya, tare da ba wa matatar damar fitar da rarar da ta wuce bukatar ƴan ƙasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng