"Ina Rokon Ku": Sakon da El Rufai Ya Turowa 'Yan Najeriya kafin a Tsare Shi

"Ina Rokon Ku": Sakon da El Rufai Ya Turowa 'Yan Najeriya kafin a Tsare Shi

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi jawabi ga ’yan Najeriya a cikin wani bidiyo d kafin ya amsa gayyatar hukumar EFCC
  • El-Rufai ya bayyana cewa yana tsammanin yiwuwar tsare shi yayin da zai bayyana a gaban EFCC, don haka ya zaɓi ya yi magana kai-tsaye da ’yan Najeriya kafin hakan ta faru
  • Tsohon gwamnan da aka taso ya buƙaci ’yan ƙasa da su kiyaye doka, su warware saɓani cikin lumana, kuma su dogara ga hukumomin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani bidiyo ya bayyana wanda ya nuna Nasir Ahmad El-Rufai na jawabi ga 'yan Najeriya kafin ya amsa gayyatar hukumar EFCC.

A cikin bidiyon, El-Rufai ya jaddada mahimmancin bin doka da kiyaye zaman lafiya a kowane fanni na rayuwa domin dorewar dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango; Dan El Rufai ya tona makarkashiyar ICPC kan mahaifinsa, ya yi zarge zarge

El-Rufai ya turo sako ga 'yan Najeriya
Nasir El-Rufai lokacin da yake shirin amsa gayyatar hukumar EFCC Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Mai magana da yawun bakin El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ne ya sanya bidiyon a ranar Lahadi, 1 ga watan Maris 2026 a shafinsa na X.

Nasir El-Rufai ya yi hasashen za a tsare shi

Yayin da yake magana kai-tsaye ga kyamara, ya bayyana cewa yana ji a jikinsa za a tsare shi na wani lokaci mai tsawo.

“Eh, yayin da nake barin gida na domin amsa gayyatar EFCC, na san sarai cewa akwai yiwuwar a tsare ni, kuma hakan na iya ɗaukar lokacin da ba a san iya tsawonsa ba."
"Saboda haka, na ga ya dace na bar muku wasu saƙonni domin mu ci gaba da tattaunawa.”

- Nasir El-Rufai

Wane sako El-Rufai ya ba 'yan Najeriya?

A saƙonsa, El-Rufai ya nanata cewa bin doka da zaman lafiya su ne jigon ci gaban kowace al'umma.

Ya tunatar da 'yan Najeriya cewa ya kamata a warware saɓani ta hanyoyin da suka dace maimakon amfani da tashin hankali.

Kara karanta wannan

Macron ya fadi shirin da Faransa ke yi bayan Amurka da Isra'ila sun kai wa Iran hari

“Bai dace kowa ya ɗauki doka a hannunsa ba. Ya kamata mu bi doka. Ya kamata mu kasance masu bin doka da oda a kowane lokaci. Idan muna da saɓani, saɓani na kashin kai ya kamata a kai shi kotu; idan kuma na jama’a ne, gwamnati za ta sa baki."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai na son a mutunta hukumomin tsaro

Haka kuma, El-Rufai ya buƙaci ’yan Najeriya da su dogara ga ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro wajen warware rikici, tare da ƙalubalantar waɗannan hukumomin su inganta ayyukansu.

“Haka ne, mutane na iya yin korafi game da ’yan sanda, amma su ne kawai ’yan sandan da muke da su. Don haka ya kamata mu yi aiki don ganin sun inganta."
"Ya kamata mu ƙalubalanci ’yan sanda su zama inganta ayyukansu, ya kamata mu ƙalubalanci sauran hukumomin tsaro su kiyaye doka da ƙa’idodin aikinsu."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya bukaci a zauna lafiya
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya bukaci a zauna lafiya

Ya kammala da yin kira ga dukkan ’yan Najeriya da su riƙa kiyaye doka da zaman lafiya a rayuwarsu ta yau da kullum.

“Zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma, kuma za mu iya samun zaman lafiya ne kawai idan kowa ya bi doka, kuma aka samu adalci a ko’ina."

Kara karanta wannan

Saura watanni 11 zabe, Attahiru Jega ya fadi barazanar da ake fuskanta a Najeriya

“Ina so na yi kira ga dukkan ’yan Najeriya da su sanya wannan a ransu a kowace rana, kowane sa’a, da kowace dakika.”

- Nasir El-Rufai

Dan El-Rufai ya magantu kan tsare mahaifinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mohammed Bello El-Rufai ya yi magana kan tsare mahaifinsa da hukumar ICPC ke ci gaba da yi.

'Dan majalisar wakilan mai wakiltar Kaduna ta Arewa ya zargi hukumar ICPC da kaddamar da yakin neman ɓata suna ga mahaifinsa, Malam Nasir El-Rufai.

Hakazalika, ya yi zargin cewa ICPC ta fi mayar da hankali kan yaƙin kafofin yaɗa labarai maimakon bin tafarkin doka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng