Zaman Tare: Fitattun Kiristocin da Suka Gina Masallatai a Najeriya

Zaman Tare: Fitattun Kiristocin da Suka Gina Masallatai a Najeriya

Ikeja, jihar Legas - Shugaban cocolin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya kaddamar da wani masallaci da ya gina a Legas.

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Primate Elijiah Ayodele ya sanya wa masallacin sunan marigayiya mahaifiyar Shugaba Bola Tinubu, Abibatu Mogaji.

Wasu fitattun Kiristoci sun gina masallatai a Najeriya
Bishop Stephen Dani Mamza da Primate Elijah Babatunde Ayodele Hoto: @primate_ayodele
Source: Twitter

Jaridar Tribune ta ce a ranar Talata, 24 ga watan Fabrairu, Folashade Tinubu-Ojo, diyar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da masallacin.

Taron ƙaddamarwar ya samu halartar mambobi da dama na al'ummar Musulmi, malaman Musulunci, da mambobin cocin Primate Ayodele, da dai sauransu.

Folasade Tinubu-Ojo ta bayyana godiyarta ga Primate Ayodele bisa gina masallacin, tana mai bayyana yunƙurin a matsayin abu mai kyau.

Ta gode wa Primate Ayodele da ya ga kakarta ta cancanci a sanya sunanta a masallacin, tana mai cewa hakan yana nuna amincewar mai wa'azin ga tasirin kakarsu.

Kara karanta wannan

Da gaske harin Iran ya hallaka Benjamin Netanyahu? an samu gaskiyar lamarin

Fitattun Kiristoci da suka gina masallatai a Najeriya

Legit Hausa ta tattaro wasu fitattun mutane Kirista waɗanda suka ba da gudunmawa wajen gina masallatai a Najeriya.

Wadannan fitattun Kiristocin dai sun hada da 'yan siyasa da kuma malaman addini, inda suka ba da gudunmawarsu ga Musulunci.

Ga jerinsu nan kasa:

1. Primate Elijah Babatunde Ayodele

A farkon watan Fabrairun 2026, Primate Elijah Ayodele ya ƙaddamar da masallacin da ya gina da kansa kuma ya sanya masa sunan marigayiya mahaifiyar Shugaba Bola Tinubu, Abibatu Mogaji.

Primate Ayodele ya gina katafaren masallaci
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Babatunde Ayodele Hoto: Primate Elijah Babatunde Ayodele
Source: Twitter

Yayin da yake jawabi a wurin taron, Primate Ayodele ya bayyana aikin a matsayin “umarni kai-tsaye daga Allah wanda ba zai iya watsi da shi ba”.

A cewar jaridar independent, Primate Ayodele ya bayyana cewa masallacin “wurin bautar Allah ne kawai”, kwatankwacin coci-coci, kuma ba shi da wani ra'ayi na kansa a cikin yadda ake gudanar da shi.

2. Gwamna Seyi Makinde

Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo wanda Kirista ne, ya tallafa wa gina masallatai da dama.

Kara karanta wannan

EFCC ta fito da Abubakar Malami, ta mayar da shi da iyalansa gaban kotu

Seyi Makinde ya gina masallaci a Oyo
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce a watan Nuwamban 2023, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya kaddamar da wani babban masallaci da Seyi Makinde ya sake ginawa.

An kaddamar da masallacin ne na Adogba da ke kan hanyar Iwo a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

3. Bishop Dani Stephen Mamza

Wani malamin addini, Stephen Dami Mamza, ya gina masallaci ga Musulmin da ke zaune a matsayin 'yan gudun hijira (IDPs) a yankin Sangere Margi na ƙaramar hukumar Girei a jihar Adamawa.

Bishop Stephen Dani Mamza ya gina masallaci
Malamin addinin Kirista, Bishop Stephen Dani Mamza Hoto: Miracle Musa
Source: Facebook

Faston wanda babban mamba ne a ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar, ya ce ya gina masallacin ne ba don wata manufa ba sai don ƙarfafa dangantaka tsakanin Musulmi da Kirista.

Yayin da yake tattaunawa da tashar ACI Africa malamin addinin ya ce:

“Duk da cewa Musulmin da ke nan kalilan ne, mun yanke shawarar gina musu masallacin tunda sun zauna a nan sama da shekaru bakwai. Cocina ne ya ɗauki nauyin dukkan aikin masallacin."

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa 9 sun rubuta wasika ga malaman musulunci, an ji abin da suka nema a Ramadan

"Amma kuma wata gidauniya daga Jamus ta gina coci, asibiti da makaranta."

- Bishop Stephen Dani Mamza

4. Martins Babale

A shekarar 2016, Martins Babale, Kirista kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Adamawa, ya gina tare da bayar da gudunmawar masallaci ga al'ummar Dalasum.

Martins Babale ya gina masallaci
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Adamawa, Martins Babale Hoto: @martins_babale
Source: Twitter

Martins Babale ya ce wannan matakin wani ƙoƙari ne na haɓaka zaman tare cikin lumana tsakanin al'ummomi daban-daban a jihar.

Ya ce ya gina masallacin ne domin inganta zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mutane mabiya addinai daban-daban.

Ya jaddada cewa zamanin rikice-rikice da rashin fahimta tsakanin mabiya addinai daban-daban ya ƙare, sannan ya nuna buƙatar zama tare cikin jituwa da fahimtar juna.

“A yau ina cika ɗaya daga cikin burina ga mutanenmu. Ina addu'ar cewa masallacin zai kuma zama cibiyar da za ta haɗa kan al'ummarmu."

- Martins Babale

Bala Lau ya bude katafaren masallaci

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kungiyar Izalah na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bude sabon masallacin Juma'a a Bichi.

Kara karanta wannan

Sheikh Murtala Asada ya yi fatali da neman yafiyar Tinubu, ya jero dalilansa

Sheikh Bala Lau ya buɗe sabon masallacin ne tare da makarantar Islamiyya da Hon. Abubakar Kabir Abubakar, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Bichi ya gina.

Katafaren Masallacin da ke kan hanyar Gwarzo a Bichi (B) ya samu sunan marigayi Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi, babban malamin addinin Musulunci kuma alkali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng