'Yan Bindiga Sun Yi Harbi a Masallaci ana Tarawihi, Sun Sace Masu Sallah a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Yi Harbi a Masallaci ana Tarawihi, Sun Sace Masu Sallah a Kaduna

  • 'Yan ta'adda dauke da makamai sun bude wuta kan wasu masu sallar tarawihi da ake a Ramadan a jihar Kaduna, inda suka sace wasu masallata
  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun bude wuta kan mai uwa da wabi kafin su samu damar sace mutanen su tafi da su cikin daji
  • Baya ga haka, wasu mazauna yankin sun shaida cewa 'yan bindigan sun shiga wasu gidaje da ke kusa da masallacin sun kama mutane

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane shida yayin da suke gudanar da sallar tarawihi a cikin wani masallaci da ke yankin Azara na karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Wani mazaunin Azara mai suna Tanimu Ibrahim ya bayyana wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta wuce.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace mahaifin tsohon mataimakin gwamna a Najeriya

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An sace masu tarawihi a Kaduna

Daily Trust ta rahoto Tanimu Ibrahim bayyana cewa ‘yan bindigan sun kutsa cikin masallacin tare da harbe-harbe kafin su yi awon gaba da mutane shida — maza hudu da mata biyu.

Tanimu ya kara da cewa yayin da suke tserewa daga yankin, ‘yan bindigar sun kuma kai farmaki wani gida inda suka sace wasu mutum biyu, amma daga bisani wadannan mutanen sun kubuta yayin da ake tafiya da su daji.

“An kuma sace wasu mutum biyu, amma da yardar Allah sun tsallake rijiya da baya yayin da ake kan hanyar shigar da su cikin daji,”

- Inji shi

Sunayen wadanda aka sace

Wani jagoran al’umma wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da sace mutanen tare da bayyana sunayensu kamar haka: Saifullahi Harisu, Yakubu Yunusa, Abba Minkailu, Yusha’u Sadiku, Maryam Abdullahi da Aisha Yakubu.

Jagoran ya kuma bayyana cewa masu garkuwar sun tuntubi al’umma da safiyar Juma’a inda suka nemi kudin fansa na Naira miliyan 30 domin sakin wadanda aka sace.

Kara karanta wannan

Mutane sun mutu ana azumi, wasu da yawa sun jikkata yayin karbar Zakka a Katsina

Ya ce:

“Sun tuntubi jama'a da misalin karfe 11:00 na safe a ranar Juma’a lokacin da shugaban ‘yan bindigar ya kira tare da neman Naira miliyan 30 sannan nan take ya kashe wayar,”
Uba Sani na bayani a wani taro a Kaduna
Gwamnan Kaduna yana jawabi a wajen taro. Hoto: Kaduna State Government
Source: Facebook

Akwai bayani daga 'yan sandan Kaduna?

Wata majiya ta ‘yan sanda a yankin ta tabbatar da sace mutanen, amma ta ki bayar da karin bayani, tana mai cewa a tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai yi martani ba game da lamarin.

An sace mata a jihar Sokoto

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan bindiga sun shiga karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto sun sace mutane, galibinsu mata.

Wasu mazauna yankin sun tabbatar da sace matan tare da sanar da cewa wasu daga cikinsu na da juna biyu, wasu kuma suna shayarwa.

Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan ta'addan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 1:00 na dare suna harba makamai kafin su sace matan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng