An Yi Yunkurin Hallaka Tinubu Ta Hanyar Sanya Masa Guba a abinci? Gaskiya Ta Fito

An Yi Yunkurin Hallaka Tinubu Ta Hanyar Sanya Masa Guba a abinci? Gaskiya Ta Fito

  • Fadar Shugaban Ƙasa ta yi magana kan jita-jitar da ke yawo cewa an sanya wa abincin shugaba Bola Tinubu guba
  • Sanarwar ta musanta cewa masu girkin fadar shugaban kasa sun yi yunkurin hallaka shi ta hanyar guba wanda ya tayar da hankula
  • Fadar shugaban kasa ta bukaci jama’a su yi watsi da rahoton, tana mai cewa labarin karya ne wanda babu gaskiya a ciki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta yi karin haske kan rade-radin cewa an yi yunkurin hallaka Shugaba Bola Tinubu wanda ya jawo maganganu a kasa.

Fadar shugaban kasar ta yi watsi da rahotannin da ke yawo da cewa an kama wasu masu girki bisa zargin yunkurin sanya masa guba a abinci.

Fadar shugaban kasa ta musanta sanya wa Tinubu guba
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi a wani taro da Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya shirya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya wallafa bidiyon rahoton a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Jagoran Musulunci na Iran: Mutane 5 da za su iya maye gurbin Ayotallah Khamenei

Yadda aka yi ta yada karya kan Tinubu

Bidiyon ya nuna wasu abubuwa a fadar shugaban kasa tare da murya mai bayanin cewa an kama wani shugaban girki bisa zargin shirya yunkurin guba.

Rahoton ya ce an dauki matakin ne bayan bayanan sirri sun nuna akwai wasu abubuwa masu ban shakku da suka shafi shirya abinci a wuraren da aka killace.

An kuma ce jami’an tsaro sun gaggauta daukar mataki bayan samun bayanai masu inganci kan yiwuwar barazana ga lafiyar shugaban kasa.

Bidiyon ya kara da cewa an gudanar da aikin cikin kwarewa da sirri domin kauce wa firgita jama’a tare da tabbatar da kawar da duk wata barazana.

An bayyana cewa wanda ake zargi ma’aikacin girki ne a bangaren ayyukan fadar shugaban kasa, kuma an tsare shi domin yi masa tambayoyi.

An musanta yunkurin sanya wa Tinubu guba a abinci
Shugaba Bola Tinubu zaune a wajen wani taro a fadar shugaban kasa Abuja. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Martanin fadar shugaban kasa a Najeriya

Sai dai Onanuga ya bayyana rahoton a matsayin labarin karya maras tushe da ake yada wa domin rudani.

Kara karanta wannan

An so zuga malami ya fito takara, shehi ya yi kaca kaca da aka ce ya nemi gwamna

Ya ce babu wani ma'aikaci da aka kama a fadar Aso Rock da zargin sanya guba a abinci inda ya shawarci jama'a da suka rika kula da irin wadannan masu yada jita-jita.

Ya ce:

“Babu wani ma’aikaci da ke girki a Aso Rock da aka kama. Babu wanda ya yi yunkurin sanya guba a abincin Shuaaba Tinubu. Ku yi watsi da wannan labarin karya.”

Har zuwa yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da karin bayani kan asalin bidiyon ko dalilin da ya sa ake yada shi ba duk da cewa hadimin Tinubu ya yi fatali da lamarin.

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan fadan Iran, Isra'ila

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargadin tsaro ga ’yan Najeriya mazauna Iran da kasashen Gulf ana tsaka da rigima.

Wannan sanarwa ya biyo bayan kai hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran da ya tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce tana sa ido kan rikicin da ke kara kamari, tare da shawartar jama’a su guji wuraren sojoji da taruka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com