Sheikh Ahmad Gumi Ya Yi Martani kan Kisan Jagoran Addinin Iran, Imam Khamenei

Sheikh Ahmad Gumi Ya Yi Martani kan Kisan Jagoran Addinin Iran, Imam Khamenei

  • Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan kisan jagoran addinin kasar Uran, Imam Ayatollah Ali Khamenei
  • Babban malamin addinin da ke zaune a Kaduna ya bayyana Khamenei a matsayin mai sa'a, wanda ya rasu wajen kare mutanen da ake zalunta
  • Gwamnatin Iran ta tabbatar da rasuwar jagoran juyin juya hali na kasar, Imam Khamenei a harin da Amurka ta kai da safiyar jiya Asabar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Fitaccen malamin addinin Musulunci da ke zaune a Kaduna, Ahmad Gumi, ya mayar da martani kan kashe jagoran addini na kasar Iran, Imam Ayatollah Ali Khamenei.

Babban malamin, wanda ke bin tafarkin Sunnah a Najeriya, ya bayyana marigayi Imam Khamenei a matsayin “mai sa'a” wanda ya rasu yana gwagwarmayar kare wadanda ake zalunta.

Kara karanta wannan

Khamenei da manyan shugabannin tsaron Iran 4 da suka rasu, ya rasa wasu iyalansa

Jagoran Iran.
Jagoran addinin musulunci na kasar Iran, Imam Ayatollah Khamenei Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wani sako da Sheikh Ahmad Gumi ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar yau Lahadi, 1 ga watan Maris, 2026.

Wanan na zuwa ne bayan kafar yada labarai mallakin gwamnatin Iran ta tabbatar da rasuwar Imam Khamenei, wanda aka ce ya ransa ne sakamakon hare-haren Amurka da Isra'ila.

Sheikh Gumi ya yi magana kan kisan Khamenei

Da yake martani kan wannan kisa, Sheikh Gumi ya ce mutuwar Khamenei ta faru ne a abin da ya kira “jihadi kan masu kashe kananan yara da mata marasa laifi a Gaza da sauran wurare”

“Mutum ne mai sa'a, ya mutu a jihadi kan masu kashe kananan yara da mata marasa laifi a Gaza da sauran wurare,” in ji Malam Ahmad Gumi.

Malamin musuluncin ya kara da cewa jinin marigayin “zai kara ruruta wutar sauyi a cikin al’umma,” yana mai cewa Imam Khamenei “ya tsaya tsayin daka wajen adalci kuma bai buya a wuraren boyo ba”

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Iran bayan rasuwar jagoran addini, Ayatullah Ali Khamenei

Gumi ya tura sako ga Amurka da Isra'ila

Sheikh Ahmad Gumi ya kuma tura sako ga wadanda suka kashe jagoran Iran, yana mai cewa su ma ba dawwama za su yi a duniya ba.

“Ga wadanda suka kashe shi ko suka taimaka wajen kashe shi, bari mu ga abin da za su rayu su aikata a wannan duniya," in ji shi.

Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya yi shekaru da dama yana rike da mukamin Jagoran Addini na Gwamnatin Musulunci ta Iran, ya kasance daya daga cikin manyan jagororin siyasa da addini a kasar.

Sheikh Gumi da Imam Khamenei.
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi da marigayi jagoran Iran, Imam Ayatolla Ali Khamenei Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Rahoton kashe shi ya haifar da martani daga sassa daban-daban na duniya, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan tasirin lamarin a harkokin siyasa da addini a yankin da ma duniya baki daya.

Dubban mutane sun yi cincirindo a Iran

A baya, kun ji cewa dubban mutane sun taru a tsakiyar birnin Tehran bayan rahoton kisan Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a harin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Jagoran Musulunci na Iran: Mutane 5 da za su iya maye gurbin Ayotallah Khamenei

Rahotanni sun nuna cewa mutanen, wadanda suka fara juyayin ruwra babbam jagoransu sun taru ne a dandalin Enghelab (Juyin Juya Hali) a ranar Lahadi, sanye da bakaken kaya.

Tuni dai gwamnatin Iran ta ayyana zaman makokin kwanaki 40 bisa rasuwar Khamenei, kuma ta sha alwashin daukar mataki mai tsanani domin ramuwar gayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262