Najeriya Ta Tafka Babban Rashi: Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Bar Duniya
- Gwamnatin jihar Delta ta fitar da wata sanarwa inda take jimami da tura sakon ta'aziyya bayan samun labarin mutuwar tsohon mataimakin gwamna
- Gwamna Sherrif ya bayyana rasuwar tsohon mataimakin gwamna a matsayin babban rashi ga jihar da kasa baki daya
- Marigayin ya taba zama mataimakin gwamna a lokacin mulkin James Ibori daga shekarar 1999 zuwa 2007 karkashin jam'iyyar PDP
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon mataimakin gwamna da aka taba yi a jihar.
Marigayin mai suna Chif Benjamin Elue, wanda ake yabon halayensa ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 85 a duniya.

Source: Facebook
An yi rashin tsohon mataimakin gwamna
Hakan na cikin sakon ta’aziyya da Babban Sakataren Yada Labaransa, Sir Festus Ahon, ya fitar wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar 28 ga watan Fabrairun 2026.
Gwamnan ya ce ya samu labarin rasuwar cikin kaduwa da radadi, amma tare da godiya ga Allah kan rayuwa mai cike da hidima da marigayin ya yi wa Delta da Najeriya.
Oborevwori ya bayyana marigayin a matsayin dan kishin kasa, gogaggen mai ma'aikaci, kuma jajirtaccen dan jam’iyya wanda gudunmawarsa za ta ci gaba da kasancewa a tarihi.
Marigayin ya taba rike mukamin mataimakin gwamna a zamanin mulkin James Ibori tsakanin 1999 zuwa 2007, lokacin da ake kokarin karfafa dimokuradiyya a farkon jamhuriya ta hudu.

Source: Twitter
Gudunmawar da marigayin ya ba al'umma a rayuwarsa
Oborevwori ya ce rayuwar Elue mai cike da gaskiya da kima ta jawo masa girmamawa a bangarorin siyasa, yana mai addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya kuma bai wa iyalansa da daukacin al’ummar Delta hakurin jure wannan babban rashi.
Gwamnan ya tuna da yadda aka san Elue da tawali’u, jajircewa da kuma biyayya ga gwamnatin da ya yi wa aiki, yana mai cewa hikimarsa ta taimaka wajen karfafa hadin kai da zaman lafiya a Delta.
Sanarwar ta ce:
“Cif Benjamin Elue mutum ne mai mutunci da gaskiya wanda ya yi wa jiharmu ƙaunatacciya hidima da ƙwazo da aminci.
"Ayyukansa masu matuƙar muhimmanci ga Delta da al’ummarta za su ci gaba da kasancewa abin tunawa har abada.”
Ya kara da cewa marigayin ba kawai dan siyasa ba ne, har ila yau shahararren malami ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen tarbiyyar matasa.
Ya yi masa addu'a ta musamman da neman Ubangiji ya yi masa rahama ya kuma ba iyalansa hakurin jure rashin.
Tsohon mataimakin gwamna a Najeriya ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Solomon Ewuga, tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa, kuma tsohon ministan Abuja ya rasu yana da shekara 70 a duniya.
Marigayin ya kasance jagoran siyasa, wanda ya ba da gagarumar gudunmawa wajen kafa jihar Nasarawa a Oktobar shekarar 1996.
Mutuwar Sanata Ewuga ta girgiza mutane, musamman a jihar Nasarawa, inda aka yi kira ga gwamnati ta ba da hutu don girmama shi duba da gudunmawar da ya ba al'umma.
Asali: Legit.ng

