Hukuncin Masu Cewa, "Azumi na Duka, Yau Lokaci ba Ya Gudu," a Watan Azumin Ramadan
- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa bai dace mai ibadar azumi ya zama mai korafi da nuna gajiyawa ba
- Fitaccen malamin ya amsa tambaya kan hukuncin masu fadin kalamai irinsu, yau azumi ba sauki da lokaci ba ya gudu a watan azumi
- A cewar Malam Daurawa, azumi jarrabawa ce daga Allah domin auna imanin bawa, don haka bai kamata a rika nuna gajiya da kosawa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya amsa tambaya kan masu korafin wahalar azumi, ko fatan mantuwar shan ruwa a watan Ramadan.
Wannan bayani da malamin ya yi na zuwa ne a daidai lokacin da azumin watan Ramadan ya fara nisa, bayan kammala goma ta marmari tare da shiga goma ta wuya.

Kara karanta wannan
Jingir ya yi fito na fito da shirin kafa 'yan sandan jihohi, malamin ya yi zargin munafurci

Source: Facebook
Kalaman da mutane ke fada saboda azumi
Wani mai bibiyar shafin BBC Hausa ne ya aika tamabaya kan wasu maganganu da mutane ke yi duk da suna azumi, kuma jaridar ta mika tambayar ga Sheikh Aminu Daurawa.
Matambayi mai suna, Abdul Ahmed Suraj ya ce mene ne matsayin irin wadannan maganganu da wasu ke yi a lokacin azumin Ramadana?
- Yau azumi babu sauki
- Dama a ce na manta na sha ruwa
- Lokaci ba ya gudu
Sheikh Aminu Daurawa ya ba da amsa
Sheikh Aminu Daurawa, malamin addinin musulunci kuma kwamandan rundunar Hisbah ta Kano, ya ce irin wadannan kalamai ba su dace da mai azumi ba kwata-kwata.
“Wadannan maganganu ba su dace ga mai yin ibada ba, ya rika nuna raki ko gajiya ko gazawa ta hanyar fadar irin wadannan kalamai. Mai bauta wa Allah dole sai ya yi hakuri,” in ji Sheikh Daurawa.
Babban malamin ya ja hankalin musulmai, yana mai cewa kamata ya yi watan azumi ya zama abin farin ciki ga kowa, ba mutum ya rika korafin wahala ba.
Daurawa ya ce Allah yana son tabbatar da hakikanin bayinsa masu jin tsoronsa shi yasa ya dora masu azumi, yana mai jaddada cewa bai dace a rika yin irin wadannan kalamai ba.
A cewarsa, azumi jarrabawa ne daga Allah domin auna imanin bawa, don haka bai kamata a rika nuna gajiya da kosawa ba.

Source: Facebook
Daurawa ya fadi kalaman da babu laifi a cikinsu
Ya ce kalaman da ke nuna gajiya ko kosawa “za su iya shafar ladan azumi, ko su tauye shi ko ma su rusa shi gaba daya."
Sai dai Sheikh Daurawa ya yi karin haske cewa babu laifi idan mai azumi ya ce “ana rana mai zafi” idan hakika zafin rana ya tsananta, ko kuma ya ce “na gaji” idan ya yi wani aiki mai wahala
Ya jaddada muhimmancin hakuri da kyautata niyya a wannan wata mai albarka domin samun cikakken lada daga Allah.
Sheikh Daurawa ya karbi bakuncin Shugaban APC
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ziyarci shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, Aminu Ibrahim Daurawa.
Bayan ziyarar, Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa yana da dangartaka mai kyau tsakaninsa da Sheikh Aminu Ibrahaim Daurawa tun shekarun baya.
Yilwatda ya bayyana cewa ya dauki nauyin adadin wasu dalibai a makarantar Zamzam da Sheikh Aminu Daurawa ke jagoranta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

