Gwamna Ya Shiga tsakani kan Rikicin Masallaci Tsakanin Izala da Kungiyoyi 2
- An samu rikici kan ikon mallakar masallacin Juma'a tsakanin wasu kungiyoyin addinin Musulunci a karamar hukumar Donga ta jihar Taraba
- Rikicin wanda aka yi a kwanakin baya ya jawo an samu asarar rayuka tare da kulle masallacin domin a samu zaman lafiya
- Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya cika alkawarin da ya dauka na warware rikici da ake yi kan masallacin na Juma'a
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya shiga tsakani kan rikicin masallacin Juma'a na Donga.
Gwamna Agbu Kefas ya bayar da Naira miliyan 300 domin magance tsohon rikicin da ake yi kan mallakar masallacin Juma’a na Donga, inda nan hedikwatar karamar hukumar Donga da ke kudancin jihar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce babban sakatare a ofishin kula da ƙananan hukumomi da masarautu, Godfrey Dame, ya wakilci gwamnan a wajen ba da kudin.
An yi rikici kan masallaci a Taraba
Rikicin mallakar masallacin a yankin ya yi sanadin asarar rayuka da kuma rufe masallacin da ake takaddama a kansa.
Takaddamar ta shafi mambobin ƙungiyar Izala ta Jos, Izala ta Kaduna, Ɗariƙa, da kuma majalisar Musulmi ta Donga, lamarin da ya sa ake fargabar rugujewar doka da oda.
A lokacin da rikicin ya yi tsanani, Gwamna Kefas ya ziyarci Donga inda ya gana da shugabannin addini da masu ruwa da tsaki, inda ya tabbatar musu da ƙudirin gwamnatinsa na magance rikicin da kuma haɓaka haɗin kai.
Gwamna Kefas Agbu ya shiga tsakani
A matsayin wani ɓangare na tsarin samar da zaman lafiya, gwamnan ya yi alƙawarin tallafa wa gina wuraren ibada daban-daban ga ƙungiyoyin da abin ya shafa domin hana ci gaba da rikici da kuma samar da zaman tare cikin lumana.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiga tsakanin nasa na nufin hana sake barkewar rikici tsakanin ƙungiyoyin Musulmi guda uku a yankin tare da dawo da zaman lafiya mai dorewa.
An raba waɗannan kuɗaɗen ne domin tallafa wa gina masallatan kansu ga kowane ɓangare da abin ya shafa, biyo bayan takaddama kan ikon sarrafa Masallacin Juma’ar na Donga, wanda a baya ya haddasa fargaba da matsalolin tsaro.

Source: Original
An ba da kudi ga kungiyoyin da ke rigima
Godfrey Dame ya miƙa cak na kuɗi jimillar Naira miliyan 300 ga ɓangarori ukun da ke rikicin, inda kowace ƙungiya ta samu Naira miliyan 100 domin ba su damar fara gina masallatansu, jaridar The Guardian ta kawo labarin.
Shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki a Donga sun jinjina wa wannan karamci na Gwamna Kefas wajen cika alƙawarin da ya ɗauka.
Gwamna Kefas ya magantu kan tazarcen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa ba zai fuskanci wata matsala wajen samawa Shugaba Bola Tinubu kuri'u a jihar Taraba ba.
Ya jaddada cewa dabarunsa na tsohon jami'in soja sun ba shi damar tsara taswirar da za ta ba shugaba Tinubu gagarumar nasara a Taraba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

