Ana Azumin Ramadan, Kotu Ta Sake Tura Malami da Matarsa zuwa Gidan Yari
- Kotu ta soke belin tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami, matarsa da dansa saboda an canza alkalin da ke sauraron kararsu
- A zaman yau Juma'a, babbar kotun tarayya ta umarci a ajiye mata Abubakar Malami a gidan yarin Kuje kafin zama na gaba
- Duk da lauyan da ke bada kariya ya yi kokarin ganin an ba da belinsa, Joyce Abdulmalik ta ce ba za ta karbi bukatar beli da baki ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Maitama, Abuja, a ranar Juma’a, ta ba da umarnin tsare tsohon Antoni Janar Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a gidan gyaran hali na Kuje.
Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta aika da Malami tare da matarsa, Hajia Bashir Asabe, da dansu, Abubakar Abdulaziz Malami, zuwa gidajen yarin har sai an yanke shawara kan bukatar belinsu.

Source: Twitter
Rahoton Daily Trust ya ce an tsare Malami da dansa a gidan gyaran hali na Kuje, yayin da aka tura matarsa, Asabe, gidan gyaran hali na Suleja.
EFCC ta sake gurfanar da Abubakar Malami
Tun farko dai hukumar EFCC ta sake gurfanar da Malami da wasu daga cikin iyalinsa ne bayan mayar da shari’ar hannun Mai Shari'a Joyce Abdulmalik daga hannun Alkali Emeka Nwite.
Ana tuhumar su ukun ne da laifuffuka 16 da suka hada da hadin baki, boyewa, da kuma karkatar da kudaden haram da suka kai N8,713,923,759.49.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa wannan ya saba wa dokar hana fasa kwabrin kudade ta shekarar 2022, kamar yadda tashar Channels tv ta rahoto.
Malami da iyalansa sun musanta aikata laifi
A lokacin da aka fara zaman shari'a, lauyan EFCC, Chief J.S. Okutepa (SAN), ya bukaci kotun da ta karanta wa wadanda ake tuhumar sababbin tuhume-tuhumen da ake y masu.
Lauyan wadanda ake tuhuma, J.B. Daudu (SAN), bai nuna adawa da hakan ba, inda aka karanto masu gaba daya tuhume-tuhumen.
Dukkan wadanda ake tuhumar sun bayyana cewa "ba su da laifi" a dukkan laifuffuka 16 da ake zargin su da aikatawa.
Bayan nan ne lauyan EFCC ya bukaci kotun da ta sanya ranar shari'a kuma a tsare wadanda ake tuhumar a gidan yari.

Source: Facebook
Abin da ya hana bada belin Malami da matarsa
Lauyan Malami ya yi kokarin rokon kotun da ta bari su ci gaba da amfana da belin da Alkali Emeka Nwite ya ba su a baya, yana mai cewa sun cika dukkan sharuddan belin kuma ba su taba keta su ba.
Sai dai, a hukuncinta, Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa an soke belin da aka ba su a baya tun da an canza alkali da kuma kotun da ke sauraren karar.
Kotun ta ki amincewa da rokon belin da aka yi ta baki, inda ta bukaci lauyoyinsu su shigar da takarda a hukumance duba da nauyin zargin da ake musu. Daga karshe, ta dage sauraren karar zuwa ranar 6 ga Maris, 2026.
Alkali ya rabu da shari'ar Abubakar Malami
A baya, kun ji cewa an samu tsaiko a shari'ar tsohon ministan shari'a kuma Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami da gwamnatin tarayya.
Mai shari'a Obiora Egwuatu, alkali a babbar kotun tarayya dake Abuja, ya janye daga jagorantar shari'o'in da suka shafi Abubakar Malami.
Mai shari'a Egwuatu ya bayyana cewa ya yanke shawarar janye jikinsa ne saboda dalilai na kansa da kuma tabbatar da adalci a shari'ar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


