Malaman Musulunci da Suka Yi wa Tinubu Rubdugu da Ya Nemi Gafarar 'Yan Najeriya
- A farkon azumin watan Ramadan 1447 shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi 'yan Najeriya su mafa afuwa idan ya musu laifi
- Legit Hausa ta rahoto cewa shugaban kasar ya nemi gafarar 'yan Najeriya ne a wajen bude tafsirin azumi a fadar shugaban kasa
- Biyo bayan rokon shugaba Tinubu, malaman Musulunci a Najeriya sun masa raddi, wasu daga cikinsu na kalubalantar shi kai tsaye
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha rubdugu a wajen wasu malaman Musulunci game da rokon a yafe masa.
Mai girma Bola Tinubu ya nemi a masa gafara ne a lokacin da ya halarci wajen tafsirin azumi a masallacin fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa shugaban kasar ya nemi a afuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar tsaro.
1. Raddin Dr Bashir ga Bola Tinubu
Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar na cikin malaman da suka yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu raddi game da neman afuwa da ya yi.
Malamin ya bayyana cewa kamata ya yi shugaban kasa ya yi kokarin sauke hakkin da aka rataya masa tun kafin lokaci ya kure.
A wani bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook, Dr Bashir ya ce:
"An ce shugaban kasa ya ce 'yan Najeriya su yafe masa. Ai ba zancen a yafe mar ba, zancen ka ba mai hakki hakkinsa. Ofis da Allah ya baka, da Allah ya ce ka yi rahama, ka yi rahama."
2. Malami a Kaduna bai yafe wa Tinubu ba
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya bayyana cewa shi dai bai yafewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu rokon da ya yi a masa gafara ba.
Legit Hausa ta rahoto malamin ya ce:
"Shugaban kasa ya fito ya ce idan ya yi muku laifi ku yafe masa, mutum yana neman yafiya ne idan ya tuba.
"Allah ya sa malamai za su karanta masa sharudan tuba, shugaban kasa a karanta maka sharudan tuba, ba ka fitowa ka ce mu yafe maka a lokacin da ka kara kudin mai.
"Ba ka fitowa ka ce mu yafe maka bayan kakaba mana haraji, ba ka fitowa ka ce mu yafe maka ana fama da rashin magani a asibiti."

Source: Facebook
3. Sheikh Asada ya ki yafewa Tinubu
A wani labari da Legit Hausa ta wallafa, wani malamin Musulunci, Sheikh Murtala Asada ya ce ba zai yafe wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba.
Malamin ya ce:
“Ba za mu yafe ba. Ga bala’i nan an kakaba wa mutane, ga haraji an kakaba wa mutane, an janye tallafin mai. Amma duk da haka wasu suna jiran lokacin kamfen su zo su yaudare mu."
"Don Allah, yanzu sai an fada maka ne? Ba sai mu Murtala Asada mun ce a ba ka kashi ba, mutane da kansu za su ba ka kashi.”
Tinubu zai sauya kundin tsarin mulki
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta amince da sauya kundin tsarin mulkin Najeriya saboda batun 'yan sandan jihohi.
Legit Hausa ta rahoto cewa shugaba Tinubu ya umarci majalisar dattawa da ta fara daukar matakin sauyin a taron buda baki da ya yi da Sanatoci.
Tinubu ya dauki matakin da niyyar kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi Najeriya da kuma matsin lamba da wasu gwamnoni suka yi masa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


