'Yan Bindiga Sun Firgita Kauyukan Bauchi, Mutane Sun Shiga Gudun Hijira

'Yan Bindiga Sun Firgita Kauyukan Bauchi, Mutane Sun Shiga Gudun Hijira

  • Matsalar 'yan bindiga masu garkuwa da mutane na cigaba da kamari a wasu kauyukan jihar Bauchi da ke karamar hukumar Alkaleri
  • Hare-haren 'yan ta'adda ya sanya mutane da dama barin gidajensu a karamar hukumar suna gudun hijira a wasu yankunan Gombe
  • Gwamna Bala Mohammed ya ziyarci daya daga cikin wajen da 'yan jiharsa suka fake da sunan gudun hijira bayan an fatattake su a gidajensu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Mazauna kauyukan Gwana, Digare, Garin Mansur da Yalo da ke gundumar Gwana a karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi sun tsere zuwa jihar Gombe sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Bala Mohammed ta ce za ta yi iya kokarinta wajen kawo karshen rikicin domin al'umma su koma gidajensu.

Kara karanta wannan

Bayan karyata shirin komawa APC, Gwamna ya roki alfarmar gwamnatin Tinubu

Wajen 'yan gudun hijira a Bauchi
Makarantar da mutane ke gudun hijira a Bauchi. Hoto: Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Source: Facebook

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta wallafa a Facebook cewa ta samu rahoton hare-hare a yankunan kuma ta tura karin dakaru garuruwan.

Hare-haren da aka kai Bauchi

Rahoto ya nuna cewa hari na farko ya faru ne a Digare, inda aka sace mutane shida, yayin da daga baya aka ceto biyu daga cikinsu.

Hari na biyu ya faru a Garin Kwairi, inda aka sace wani kansila tare da mata biyu, ‘yan bindigar sun kuma kai hari a Gwana, inda suka kashe sojoji biyu da dan kungiyar sa-kai guda.

An fafata da 'yan bindiga a Bauchi

Sai dai, mazauna kauyen tare da jami’an tsaro sun fatattaki maharan, inda aka ruwaito cewa sun kashe ‘yan bindiga bakwai a yayin arangamar.

A wani hari da aka kai a kauyen Kafin Duguri, mutane hudu sun rasa rayukansu, duk da cewa mazauna yankin sun ce sama da ‘yan bindiga 20 ne aka kashe a fafatawar.

Kara karanta wannan

Bayan kai hari masallaci, 'yan bindiga sun sace mata masu ciki a Sokoto

'Yan Bauchi na gudun hijira a Gombe

Wasu daga cikin wadanda suka rasa muhallansu sun ce sun bar gidajensu da dukiyoyinsu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da ke cigaba da afkuwa.

Sun bayyana cewa da dama sun tsere zuwa Kumo, Gombe, Kashere, Alkaleri da sauran sassan jihar Bauchi, yayin da wasu suka nemi mafaka a jihohin Filato da Taraba.

Da suke magana a makarantar firamare da ke Kashere a jihar Gombe, mutanen da suka tsere sun ce ‘yan bindiga kan kai hari kan al’ummominsu da dare ko ma da tsakar rana.

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa 'yan gudun hijiran sun ce 'yan ta'addan suna sace shanu, wawushe dukiya tare da sace mutane domin neman kudin fansa.

Gwamna Bala Mohammed a Gwana
Bala Mohammed a yankin da ke fama da 'yan bindiga a Bauchi. Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Source: Facebook

Hadimin gwamnan Bauchi, Lawal Muazu ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da 'yan gudun hijira suka fake.

'Yan bindiga sun sace mata a Sokoto

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto sun sace mutane ciki har da mata.

Kara karanta wannan

Bala Mohammed: Yadda yan ta'adda ke kara daukar sababbin matasa a Bauchi

Mazauna yankin da aka kai harin sun koka da cewa wasu daga cikin matan da aka sace suna shayarwa wasu kuma suna da juna biyu.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da kai harin, inda ta bayyana cewa tana cigaba da tantance hakikanin abubuwan da suka faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng