Matakin da Gwamnatin Kano ta Dauka kan Dan Kwankwaso da Kwamishinonin da Suka Bar Abba
- A kwanakin baya wasu daga cikin kwamishinonin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sun yi murabus
- Bayan murabus dinsu, gwamnati ta bukaci tsofaffin kwamishinonin su dawo da motocin da suke a hannunsu
- Hukumar PCACC ta dauki mataki na gaba bayan tsofaffin kwamishinonin sun yi biris da umarnin da aka ba su na dawo da motocin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta kwato motocin gwamnati daga hannun wasu tsofaffin kwamishinoni.
Hukumar PCACC ta kwato motocin ne daga hannun kwamishinonin waɗanda ake zargi da kin mayar da su bayan sun yi murabus daga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce shugaban hukumar PCACC, Saidu Yahaya, wanda ya jagoranci aikin kwato motocin a ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026, ya bayyana cewa an samu motoci biyar, mota ɗaya daga hannun kowane tsohon kwamishina.
Tsofaffin kwamishinonin, waɗanda masu biyayya ne ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi murabus ne biyo bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.
An kwato motoci a hannun tsofaffin kwamishinoni
A cikin waɗanda aka kwato, guda biyu motocin gwamnati ne na asali, yayin da sauran guda ukun ba su ba ne.
Ya ce hukumar tana da niyyar gudanar da bincike ko an sayar da motocin ne ko kuma tantance matsayin da suke ciki a yanzu, shafin Solacebase ya kawo labarin.
“Kwamishinoni biyar ne suka yi murabus daga ayyukansu a wannan gwamnati kwanan nan. Akwai motocin da aka ba su, kuma an ba su shawarar su mayar da su, amma suka yi kunnen uwar shegu da umarninmu."
"Mun bi hanyoyin da doka ta tanada kuma mun samu izinin kotu domin ƙwato motocin."
"Ya zuwa yanzu, mun karɓo motoci biyar daga hannun kwamishinonin. A cikin waɗannan, biyu motocin gwamnati ne, sauran ukun kuma ba su ba ne. Ana zargin cewa an sayar da motocin ne domin sayen waɗannan."
"Za mu gudanar da bincike don tantance ko an sayar da motocin gwamnatin ne aka sayi waɗannan, ko kuma mu san matsayinsu.”

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Kwankwasiyya ta nuna yatsa ga Gwamna Abba kan zargin muzgunawa 'yan adawa
- Saidu Yahaya
Tsofaffin kwamishinoni sun ki dawo da motoci
Saidu Yahaya ya bayyana cewa kafin ƙwato motocin, gwamnati da hukumar sun rubuta wasiƙu zuwa ga tsofaffin kwamishinonin suna buƙatar su mayar da motocin, amma suka yi watsi da wasiƙun.

Source: Facebook
An ƙwato motocin ne daga hannun tsoffin kwamishinoni kamar haka:
- AVM Ibrahim Umar: Tsohon kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman
- Mustapha Rabiu Kwankwaso: Tsohon kwamishinan matasa da wasanni
- Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata: Tsohon kwamishinan kimiyya, fasaha
- Dr. Adams Aliyu Kibiya: Tsohon kwamishinan al’amuran jin kai
- Hon. Nasiru Sani Garo: Tsohon kwamishinan ayyuka na musamman
Gwamnatin Kano ta musanta cin zarafin 'yan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta yi martani kan zargin cin zarafin 'yan adawa.
Gwamnatin ta yi watsi da zarge-zargen da ke cewa tana kamawa, tsarewa, da cin zarafin mutanen da ke sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hakazalika, ta jaddada cewa jama'a na da ’yancin bayyana ra’ayoyinsu kan shugabanci ba tare da cin zarafi ba.
Asali: Legit.ng
