Ana Wata ga Wata: El Rufai Na Tsare, an Kunno Masa Sabuwar Wuta a Kaduna

Ana Wata ga Wata: El Rufai Na Tsare, an Kunno Masa Sabuwar Wuta a Kaduna

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai na ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci ta ICPC
  • Yayin da tsohon gwamnan yake ci gaba da zama a tsare, wasu mutane sun fito kan tituna domin gudanar da zanga-zanga a Kaduna
  • Sun bukaci a gudanar da bincike kan yadda tsohon gwamnan ya gudanar da mulkinsa da kuma wasu basussuka da ya karbo a jihar

​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Mazauna jihar Kaduna sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a gidan gwamnati kan Nasir El-Rufai da ta wuce.

Masu zanga-zangar sun buƙaci amsoshi kan ɓatan Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, tare da yin kira ga a gudanar da bincike kan mulkin tsohon gwamna Nasir El-Rufai.

An yi zanga-zangar neman a binciki Nasir El-Rufai
Nasir El-Rufai da masu zanga-zangar neman a bincike shi a Kaduna Hoto: @elrufai, @flexiblenancy
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce masu zanga-zangar, waɗanda suka haɗa da maza da mata, sun taru ne a mahadar UTC da ke tsakiyar birnin Kaduna kafin su nufi fadar gwamnati a ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

An samu matsala, kotu ta yi watsi da bukatar belin El Rufai saboda wani dalili

An yi zanga-zanga kan Nasir El-Rufai

Masu zanga-zangar sun rika rera waƙoƙin haɗin kai sannan suna ɗauke da alluna masu rubutu daban-daban.

Wasu daga cikin allunan na dauke da rubutu kamar: “Muna buƙatar binciken kuɗi yanzu,” “Malam Nasir El-Rufai, ina Dadiyata yake?” da kuma “A wallafa yarjejeniyar bashi da bayanin yadda aka kashe kuɗaɗen yanzu.”

Wasu saƙonni kuma sun haɗa da “Kaduna ta rayu cikin tsoro, muna son gaskiya,” da kuma “Shirya zanga-zanga ba zai kare El-Rufai ba; dole ne ya fuskanci shari’a.”

Meyasa aka yi zanga-zangar?

Yayin da yake jawabi ga manema labarai lokacin zanga-zangar, ɗaya daga cikin shugabannin masu tattakin, Anas Yusuf, ya bayyana cewa wannan yunƙuri ba na siyasa ba ne, manufarsa ita ce neman gaskiya.

“Ba mu zo nan don siyasa ba; muna nan ne don neman gaskiya. Kaduna ta sha wuya. An kai wa al’ummomi hari, yankin Birnin Gwari ya fuskanci matsaloli, ayyukan 'yan bindiga sun ƙaru, an yi garkuwa mutane, iyalai sun binne masoyansu, sannan tsoro ya zama ruwan dare lokacin gwamnatin da ta gabata."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano da Ganduje sun buga muhawara mai zafi a kotu kan zargin almundahana

"Waɗannan shekarun ba za a goge su da jawabi ba. Dole ne tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya amsa tambayoyi. Ka yi mulki, yanzu kuma dole ne ka bayar da bayani."

- Anas Yusuf

An yi zanga-zanga kan El-Rufai a Kaduna
Masu zanga-zangar neman a binciki El-Rufai a Kaduna Hoto: @flexiblenancy
Source: Twitter

An bukaci a binciki basussukan El-Rufai

Haka kuma, sun yi kira da a fito fili a bayyana gaskiya game da bashin dala miliyan 350 da aka karɓo daga Bankin Duniya a zamanin tsohon gwamnan, jaridar The Guardian ta kawo labarin.

Sun buƙaci gwamnatin jihar da ta wallafa takardun yarjejeniyar bashin da kuma bayani filla-filla kan yadda aka rarraba kuɗaɗen.

MURIC ta bukaci a saki Malam El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta nuna damuwa kan ci gaba da tsare Malam Nasir El-Rufai.

Kungiyar MURIC ta yi Allah-wadai da ci gaba da tsare tsohon gwamnan na jihar Kaduna, da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ke yi.

Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya buƙaci a saki El-Rufai cikin gaggawa ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng