An Yi Hasashen Tinubu Zai Yi Garambawul, Zai Shafi Hafsan Sojoji, Manyan Jami’ai

An Yi Hasashen Tinubu Zai Yi Garambawul, Zai Shafi Hafsan Sojoji, Manyan Jami’ai

  • Fasto Ayodele ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi wasu manyan sauye-sauye a gwamnatinsa kafin karshen 2026
  • Ya ce sauyin shugabannin tsaro na da nasaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasa na 2027 da ake tunkara a Najeriya
  • Malamin ya gargadi shugabannin tsaro su shirya, yana mai cewa hukuncin ya riga ya tabbata sai dai idan Allah ya sauya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele, ya yi hasashe a gwamnatin Bola Tinubu game da garambawul.

Primate Ayodele ya bayyana cewa za a samu gagarumin sauyi a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kafin karshen shekarar 2026.

Fasto ya yi hasashen garambawul a gwamnatin Tinubu
Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar, wanda PM News ta samu.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu ya sanar da sabon shugaban 'yan sanda yayin rantsar da shi

Ayodele ya kira sunan Hafsan Sojoji da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, wanda daman shi kam ya yi murabus, cewa za a cire su daga mukamansu kafin zaben 2027.

Yadda shugaban yan sanda ya yi murabus

Wannan hasashe na Ayodele na zuwa a ranar da aka sanar da murabus din Sufeta-janar na yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun wanda ya jawo maganganu a Najeriya.

Murabus din Egbetokun na zuwa ne bayan ya gana da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Litinin 24 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.

Yan Najeriya da dama sun nuna damuwa game da murabus din, inda suke zargin tilasta masa aka yi ya ajiye aikin duba da zarge-zarge da ake yi masa.

Hasashen Fasto ya tabbata a Najeriya
Babban Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele. Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele.
Source: Twitter

Hasashen garambawul da Fasto Ayodele ya yi

Malamin ya bayyana cewa sauyin yana cikin shirye-shiryen sake fasalin manyan hukumomin tsaro domin daidaita tafiyar gwamnati gabanin babban zaben shugaban kasa mai zuwa.

“Ubangiji ya bayyana min cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olukayode Egbetokun, Hafsan Sojoji da wasu shugabannin hukumomin tsaro za a cire su daga mukamansu kafin karshen shekarar nan.

Kara karanta wannan

Bayan maganganu sun yi yawa, Tinubu ya yi bayani kan murkushe adawa a Najeriya

“Shugaban kasa zai aiwatar da wadannan sauye-sauye kafin zabe, sai dai idan Allah ya sauya shawara. An riga an yanke hukunci. Su shirya wanzuwar wannan mataki.”

Ayodele ya sha jan hankalin yan Najeriya

Ayodele ya taba jan hankalin jama’a tun kafin zuwa wannan gwamnati cewa wata gwamnatin APC za ta jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Haka kuma ya nuna cewa gwamnatin mai ci na fuskantar kalubale wajen samun cikakken girmamawa a kasashen waje, daidaita tattalin arziki da kuma gamsar da jama’a kafin zaben 2027.

Shugaban yan sandan Najeriya ya yi murabus

An ji cewa rahotanni daga fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa Bola Tinubu ya umarci Sufeto-janar na Yan Sandan Najeriya ya yi murabus.

Majiyoyi daga hedkwatar rundunar yan sanda sun tabbatar da lamarin, sun ce an fara shirin mika ragamar mulki ga wani daga cikin mataimakansa.

Fadar ta ce Egbetokun ya yi murabus ne domin samun damar kula da iyalansa wanda tuni shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da haka tare da nada sabon shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.