Majalisar Dattawa Ta Dauki Zafi, Ta Bukaci Shugaba Tinubu Ya Tsige Shugaban CAC
- Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin tsige shugaban hukumar CAC, Hussaini Ishaq Magaji (SAN)
- Kwamitin majalisar mai kula da harkokin kudi ne ya dauki wannan matsaya a zamansa na ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairu, 2026 a Abuja
- Ya zargi Magaji da kin amsa gayyatar da majalisar ta tura masa sau da dama domin ya bayyana yadda ake tafiyar da kudaden hukumar da yake jagoranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar dattawan Najeriya ta fusata bisa rashin girmanawa takardun gayyatar da ta aika wa Shugaban Hukumar Yi wa Kamfanonin Masu Zaman Kansu Rajista (CAC), Hussaini Ishaq Magaji (SAN).
Rahotanni sun nuna cewa majalisar ta gayyaci shugaban CAC na ka kasa sau da dama domin ya bayyana a gabanta, amma har yanzu bai amsa ko daya daga ciki ba.

Source: Facebook
Bisa haka ne Majalisar Dattawan ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya tsige Shugaban Hukumar CAC, Hussaini Ishaq Magaji (SAN), daga mukaminsa, kamar yadda jaridar Tribune Nigeria ta kawo.
Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kudade, ne ya yanke wannan shawara a zamansa na ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026 a birnin tarayya Abuja.
Sanata Orji Uzor Kalu ya gabatar da kudirin neman tsige shugaban CAC a lokacin da tawagar tattalin arziki ta Shugaban Kasa ta bayyana a gaban kwamitin.
A lokacin gabatar da shugabannin hukumomin da suka amsa gayyata, ’yan majalisar sun nuna bacin ransu kan rashin zuwan shugaban hukumar CAC, wanda aka gayyata domin ya yi bayani.
Cike da fushi, Sanata Uzor Kalu ya mika bukatar a gaggauta tsige Magaji daga shugabancin CAC, inda ya bayyana abin da taurin kai wajen kin amsa gayyatar kwamitin kudi.
"Tun da na zo Majalisar Dattawa, ko da yaushe yana bayar da uzurin iri daya cewa yana fadar shugaban kasa.”
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kudade, Sanata Sani Musa, shi ma ya nuna damuwarsa game da wasu matsaloli da ba a warware ba dangane da tantance kudaden shiga na CAC.
Ya koka kan yadda shugaban hukumar CAC ya ki amsa duka gayyatar da aka masa ya bayyana domin magance wadannan batutuwa.
Da yake goyon bayan bukatar, Sanata Adams Oshiomhole ya ba da shawarar cewa majalisar ta dauki karin matakai ta hanyar kin amincewa da kasafin kudin hukumar CAC na shekarar 2026.
Daga karshe dai, an amince da wannan bukatar ta neman Shugaban Kasa ya tsige shugaban na CAC.
Asali: Legit.ng

