Musulunci Ya Samu Karuwa, An Tabbatar da Musuluntar Fitaccen Mawaki a Najeriya

Musulunci Ya Samu Karuwa, An Tabbatar da Musuluntar Fitaccen Mawaki a Najeriya

  • Abokin fitaccen mawakin Najeriya, Burna Boy ya tabbatar da musuluntarsa a wani gajeren sako da ya fitar yau Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026
  • Rahman Jago ya bayyana cewa mawaki Burna Boy ya karbi shahada kuma yanzu yana bin koyarwar addinin musulunci a rayuwarsa
  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya taya shi murna tare masa fatan alheri da dacewa a addinin musulunci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - An kara tabbatar da labarin cewa fitaccen mawakin nan na Najeriya, Burna Boy, ya yi kalmar shahada ya karbi addinin musulunci.

A kwanakin baya, aka yada rahoton cewa Burna Boy, wanda yana daya daga cikin mawakan da tauraruwarsu ke haskawa, ya karbi addinin musulunci.

Mawaki Burna Boy.
Fitaccen mawakin Najeriya da tauraruwarsa ke haskawa, Burna Boy
Source: Instagram

Rahman ya tabbatar da musuluntar Burna Boy

Yayin da ake ci gaba da azumin watan Ramadan, Rahman Jago, abokin shahararren mawakin ya tabbatar da musuluntar Burna Boy a shafinsa na X ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

An yi hasashen Tinubu zai yi garambawul, zai shafi hafsan sojoji, manyan jami'ai

Rahman ya ce mawakin, wanda ya taba lashe kyautar Grammy, ya bar addinin Kiristanci tare da komawa Musulunci.

Har ila yau, ya wallafa wani bidiyo na Burna Boy yana ambaton Allah (SWT) a shafinsa, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma tattaunawa mai zafi a tsakanin masoya mawakin da mabiyansa.

Bashir Ahmad ya taya Burna Boy murna

Bashir Ahmad, tsohon hadimi ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci kan bidiyon da aka ga Burna Boy yana yabon Allah.

Bashir ya bayyana mawakin a matsayin wanda yake "cikin farin ciki" sannan ya taya shi murna da addu'ar fatan alheri a addinin Musulunci: "Allah (SWT) ya saukaka masa."

Yayin da wani masoyin mawakin ya tambayi Bashir Ahmad ko da gaske ne Burna Boy ya musulunta, ya amsa da cewa wasu daga cikin makusantan mawakin sun yi ikirarin cewa ya musulunta.

Amma har yanzu, Burna Boy da kansa bai fito ya tabbatar da hakan a hukumance ba tukuna, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

Kara karanta wannan

An rikita malaman Musulunci da miliyoyi a Kaduna, sun nuna goyon bayansu ga APC

Burna Boy.
Shahararren mawakin Najeriya da ya ci kyautar Grammy, Burna Boy Hoto: Burna Boy
Source: Instagram

Burna Boy ya karbi shahada

Sai dai, Rahman Jago ya fito fili ya tabbatar da cewa Burna Boy ya riga ya musulunta, inda ya rubuta: “Ya musulunta. Yanzu shi Musulmi ne.”

Burna Boy, wanda ya fito daga gidan Kirista, ya taba bayyana a wata hira da aka yi da shi kwanan nan cewa ya rungumi addinin Musulunci a "wani lokaci" domin neman gaskiya.

Mawakin ya sake jaddada batun musuluntar tasa yayin wani shiri kai-tsaye da ya yi da Plaueboymax, inda ya bayyana ra'ayoyinsa game da halittar duniya.

Mawakin Birtaniya, Centran Cee ya karbi Musulunci

A wani rahoton, kun ji cewa musulmai sun samu karuwa yayin fitaccen mawakin Birtaniya, Central Cee, ya sanar da karɓar addinin Musulunci tare da furta kalmar shahada.

An haifi Central Cee a ranar 4 ga watan Yuni, 1998, a birnin Landan, mahaifiyarsa ’yar Ingila ce, yayin da mahaifinsa ke zama dan asalin Guyana da China.

Mawakin da aka fi sani da sunan Oakley Neil Caesar-Su ya fito ya tabbatarwa mabiyarsa cewa ya karbi kalmar shahada wanda ke tabbatar da ya koma addinin Musulunci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262