Kotu a Amurka Ta Yanke Wa Tsohon Jami’in NNPCL Hukunci kan Cin Hancin $2.1m
- Wata kotu a kasar Amurka ta yanke wa tsohon jami’in NNPC hukuncin daurin watanni 87 kan cin hancin Dala miliyan 2.1
- An same shi da laifin halatta kudin haram da kuma kauce wa biyan haraji da kuma hana bincikensa da aka fara
- Hukumar lauyoyi ta Jihar California ta dakatar da lasisinsa a watan Janairun 2026 bayan an an kama shi da laifi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wata kotun tarayya da ke Amurka ta yankewa tsohon babban jami’in Kamfanin Mai na Kasa, (NNPC), Paulinus Okoronkwo, hukunci.
Kotun ta amince a yi daurin watanni 87 a gidan yari bisa samunsa da karbar cin hancin dala miliyan 2.1 da ke da alaka da hakkin hako mai a Najeriya.

Source: Getty Images
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Alkalin kotun tarayya, John Walter ne ya yanke hukuncin, kamar yadda ofishin Lauyan gwamnatin Amurka a California ya bayyana.
An yanke wa tsohon jami'in NNPC hukunci
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Okoronkwo mai shekara 58 yana da katin zama 'dan kasashe har biyu - Amurka da Najeriya.
A baya ya rike mukamin Babban Manajan na NNPC, sashen da ke kula da albarkatun danyen mai da iskar gas ta hanyar hadin gwiwa da kamfanonin ketare.
Kotun ta bayyana cewa a matsayinsa na jami’in gwamnati, yana da alhakin rikon amana ga gwamnatin Najeriya.

Source: Twitter
A watan Agustan 2025, alkalai sun same shi da laifuffuka uku na halatta mu'amala da kudin haram, laifi daya na kauce wa biyan haraji da kuma laifi daya na hana gudanar da binciken shari’a bayan shari’ar kwanaki hudu.
An kuma umarce shi da ya biya Dala 923,824 ga Hukumar Haraji ta Amurka (IRS) a matsayin diyya, tare da kwace Dala 1,039,997 daga kudin sayar da wani gida da aka danganta da kudin cin hancin.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Wasu manyan alkalai a Najeriya na iya shiga matsala da NJC ta fara bincikensu
Laifin da aka kama tsohon NNPCL da shi
Takardun kotu sun nuna cewa a watan Oktoban 2015, kamfanin Addax Petroleum, reshen kamfanin mai na kasar Sin Sinopec, ya tura Dala 2,105,263 zuwa asusun lauyoyi (IOLTA) na kamfanin lauyoyin Okoronkwo da ke Los Angeles.
An bayyana kudin a matsayin na shawarwari kan sulhu da NNPC dangane da hakkin hako mai. Sai dai masu gabatar da kara sun ce wannan dabara ce ta boye cin hanci.
Masu bincike sun ce kamfanin zai iya yin asarar biliyoyin Daloli idan ba a bar masa hakkin hakar mai ba. An kuma zargi kamfanin da korar wasu jami’ai da suka nuna damuwa.
Daga 2016 zuwa 2018, Okoronkwo ya rika tura kudin ta hannun wani kamfani mai suna IPO Capital LLC, yana biyan bukatun kansa.
Daga cikin abubuwan da ya yi da su akwai sayen mota da kadarori. A 2017 ya kashe kusan Dala 983,200 a matsayin kudin ajiya na wani gida a Valencia, California.

Kara karanta wannan
Bincike ya tono ministan Buhari da wani mutum sun fitar da miliyoyi a kifar da Tinubu
Tsohon shugaba a NNPCL ya shiga matsala
A baya, mun wallafa cewa wata kotun tarayyar Amurka, ta samu tsohon babban manajan kamfanin NNPCL da laifin karɓar rashawar Dala miliyan 2.1.
An samu Paulinus Okoronkwo da laifuffukan da suka haɗa da satar kuɗi, karya dokar haraji da kuma kawo tsaiko a binciken da ake yi masa na
Wannan shari'ar rashawar ta zama mai girma da ta shafi bangaren mai a Najeriya tare da kamfanonin ƙasashen waje, abin da zai iya girgiza sahihancin wannan fanni.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
