Saudiyya Ta Sanya Ranar da Za Ta Dawo Jigilar Fasinjoji tsakanin Jiddah da Abuja

Saudiyya Ta Sanya Ranar da Za Ta Dawo Jigilar Fasinjoji tsakanin Jiddah da Abuja

  • Gwamnatin Saudiyya ta bayyana lokacin da kamfanin jirgin saman kasarta zai dawo da zirga-zirga tsakanin Jeddah da Abuja
  • Jakadan ƙasar Saudiyya, Ambasada Yousef Albalawi ya bayyana hakan a ziyarar da ya kai wa ministan yada labaran Najeriya
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi uku na hadin gwiwa da kasar Saudiyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jakadan ƙasar Saudiyya a Najeriya, Ambasada Yousef Albalawi, ya bayyana cewa kamfanin jiragen saman Saudiyya zai sake dawo da jigilar fasinjoji daga Jeddah zuwa Abuja.

Ambasada Yousef Albalawi ya sanar da cewa kamfanin jiragen zai dawo da zirga zirgar ne a watan Yuni na wannan shekara ko kuma nan da watan Janairun 2027.

Saudiyya za ta dawo da jigilar fasinjoji tsakanin Jiddah da Abuja
Ambasadan Saudiyya a Najeria, Yousef Albalawi yana gaisawa da ministan yada labaran Najeriya, Mohammed Idris a Abuja. Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Saudiyya za ta saukaka wa 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta dauki zafi, ta bukaci Shugaba Tinubu ya tsige shugaban CAC

Jakadan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ya kai ziyara ga ministan yaɗa labarai da wayar da kai na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris, a Abuja, in ji rahoton Punch.

Ambasada Yousef Albalawi ya jaddada cewa ya kai ziyarar ne da nufin ƙarfafa dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannonin tattalin arziƙi, siyasa, da tsaro.

Baya ga dawo da sufurin jiragen sama tsakanin Jiddah da Abuja, jakadan ya bayyana cewa ƙasarsa za ta ci gaba da ba ƴan Najeriya dukkan goyon bayan da suke buƙata domin gudanar da aikin Hajji da Umrah cikin sauƙi.

Ya kuma bayyana aniyarsa ta yin aiki da ma'aikatar yaɗa labarai da kafafen watsa labarai domin gyara duk wani gurɓataccen bayani game da ƙasar Saudiyya.

Yarjejeniyoyin haɗin gwiwa 3

A nasa martanin, Minista Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta riga ta sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi guda uku (3) da gwamnatin Saudiyya ta nema.

A cikin sanarwar da ma'aikatar yada labaran Najeriya ta wallafa a shafinta na X, an lissafo waɗannan yarjejeniyoyi da suka haɗa da:

Kara karanta wannan

Najeriya ta cire tsoro ta karyata rahoton Amurka kan Kiristoci

  1. Musayar labarai tsakanin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da na Saudiyya (SPA).
  2. Haɗin gwiwa a fannin rediyo da talabijin tsakanin NTA da hukumar yaɗa labaran Saudiyya.
  3. Haɗin gwiwa a fannin kimiyya da fasahar yaɗa labarai tsakanin NBC da takwararta ta Saudiyya.
Saudiyya za ta dawo jigilar fasinjoji tsakanin Jiddah da Abuja a Yuni ko farkon 2027.
Jirgin kamfanin jiragen saman Saudiyya, watau Saudi Airline. Hoto: @Saudi_Airlines
Source: Twitter

Ministan Najeriya zai gana da na Saudiyya

Ministan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai gana da takwaransa na ƙasar Saudiyya domin tabbatar da cewa waɗannan yarjejeniyoyi sun fara aiki yadda ya kamata.

Wannan dai wani babban mataki ne da zai buɗe wa ƙasashen biyu kofofin ci gaba musamman ta fannin yaɗa labarai da tattalin arziƙi.

Saudiyya za ta dauki 'yan Najeriya aiki

A wani labari, mun ruwaito cewa, Saudiyya za ta ɗauki ’yan Najeriya aiki bayan yarjejeniya da aka ƙulla domin tsara daukar ma’aikata da kare haƙƙoƙinsu.

Yarjejeniyar na cikin manufofin 'Vision 2030' da Saudiyya ke aiwatarwa domin gyaran tsarin aiki da bunƙasa tattalin arzikinta.

Najeriya na ganin yarjejeniyar a matsayin dama mai muhimmanci wajen rage rashin aikin yi, tare da tabbatar da kariya da walwalar ’yan ƙasar a waje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com