Ramadan: Lakurawa Sun Bude Wuta a Masallaci, Sun Kashe Mutane ana Sallar Tarawihi

Ramadan: Lakurawa Sun Bude Wuta a Masallaci, Sun Kashe Mutane ana Sallar Tarawihi

  • Yan ta'addan Lakurawa sun kai farmaki wani masallaci yayin da mutane ke tsakiyar gudanar da sallar tarawihi a jihar Kebbi
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin, wanda ya faru a garin Dadin Kowa da ke karamar hukumar Maiyawa, ya yi ajalin mutane da dama a daren jiya Laraba
  • Babu wata sanarwa a hukumance, amma mazauna garin sun tabbatar wa Legit Hausa faruwar lamarin a watan azumin Ramadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa sun kai mummunan hari kan mutane suna tsakiyar sallar tarawihi a jihar Kebbi.

Bayanai sun nuna cewa 'yan ta'addan sun bude wa masallata wuta suna cikin sallah a daren jiya Laraba a garin Dadin Kowa da ke yankin karamar hukumar Maiyama ta jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi kazamin fada da Boko Haram, an zubar da jinin 'yan ta'adda

Jihar Kebbi.
Taswirar jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani mai amfani da kafar sada zumunta ta X, Bakatsine, wanda ya saba kawo labaran matsalar tsaro, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa da safiyar yau Alhamis.

Lakurawa sun kashe mutane a masallaci

Ya ce maharan sun far wa mutanen suna tsaka da sallar tarawihi, ibadar da musulmi ke yi a watan azumin Ramadan domin neman yardar Allah SWT.

Rahoto ya nuna cewa an kashe mutane da dama, wasu da yawa kuma sun jikkata, sannan an keta alfarmar masallaci wanda yake matsayin wuri mai tsarki ga musulmi.

"A daren jiya, wasu mayakan Lakurawa sun far wa al’ummar garin Dadin-Kowa da ke karamar hukumar Maiyama a Jihar Kebbi, inda suka kai hari kan mazauna garin yayin da suke gudanar da sallar Tarawihi.
"A harin, an kashe mutane da dama, wasu da yawa kuma sun jikkata, sannan an keta alfarmar masallaci wanda yake matsayin wuri mai tsarki."

Kara karanta wannan

Amnesty ta hurawa Abba Kabir wuta a Kano, ta zarge shi da cin zarafin 'yan adawa

An tabbatar da mutuwar mutum 4

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na X.

Ya ce mutane hudu ne suka rasa rayukansu a harin, wanda ake zargin mayakan Lakurawa sun kaddamar domin daukar fansar abin da sojoji suka masu.

"Majiyoyi sun ce maharan sun kutsa garin, suka bude wuta kan masallata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, yayin da wasu biyar suka samu raunuka daban-daban.
"An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti domin neman magani," in ji Zagazola Makama.

An kashe 'dan agajin Izala a harin

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin Legit Hausa, ya ce ba a kammala tantance yawan wadanda suka mutu ba.

Matashin ya tabbatar da cewa abokinsa, 'dan agajin JIBWIS na cikin wadanda aka kashe a harin, inda ya yi addu'ar Allah Ya karbi shahadarsa.

Kara karanta wannan

Amurka: Ɗan bindiga ya tare limamin masallaci, ya bude masa wuta da bindiga

Gwamna Nasir Idris.
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook
"A daren jiya ne Lakurawa suka kashe abokina a masallaci, na samu labarin 'yan uwa da dama sun rasa rayukansu, muna rokon addu'o'in ku, Allah Ya jikanshi Ya gafarta mashi da dukkan musulmi," in ji shi.

Sojoji sun dakile harin mayakan Lakurawa

A wani rahoton, kun ji cewa an gwabza fada tsakanin dakarun sojojin Najeriya da 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma.

Rahotanni sun nuna cewa an yi wannan artabu ne lokacin mayakan Lakurawa suka farmaki tawagar kwamandan rundunar Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Bemgha Koughna.

Dakarun sojojin sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan inda suka hallaka da dama daga cikinsu tare da kwato makamai da dama daga hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262